Juaboso (gunduma)
Juaboso | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | ||||
Yankuna na Ghana | Yankin arewa maso yamma |
Gundumar Juaboso na ɗaya daga cikin gundumomi tara a Yankin Arewa maso Yammacin kasar Ghana.[1][2][3][4][5][6] Asali yana daga cikin Gundumar Juaboso-Bodi mafi girma a lokacin a shekara ya 2004, har sai da aka raba wani yanki na gundumar don ƙirƙirar Gundumar Bodi a ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2012; don haka aka sake canza sauran ɓangaren asali zuwa Gundumar Juaboso. Majalisar gundumar tana cikin yankin arewa maso yamma na Yankin Arewa maso Yamma kuma tana da Juaboso a matsayin babban birninta.
Garin Juaboso
[gyara sashe | gyara masomin]A kalla Yana da kimanin kilomita 65 arewa maso yamma da babban birnin gundumar Wiawso. Hakanan yana da nisan kilomita 360 arewa maso yamma na Takoradi a gabar Tekun Atlantika da kilomita 225km kudu maso yamma da Kumasi, babban birnin yankin Ashanti.[7]
Labarin kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Gundumar Juaboso ta kasance tsakanin latitude 6°6'N da 7°N, da kuma longitude 2°40'W da 3°15'W. Daga arewa akwai yankin Bia-East, Bia West da kuma Asunafo North Municipal District. Makwabtanta na gabas sune Asunafo ta Kudu da kuma gundumomin Bodi. Yankin Suaman yana kudu da La Cote d'lvoire yana yamma.[7]
Tsarin yanki
[gyara sashe | gyara masomin]Gundumar Juaboso tana da kananan hukumomi har hudu, Kofikrom-Proso, Asempaneye, Benchema-Nkatieso da Boinzan.
Yawan jama'a
[gyara sashe | gyara masomin]Yawan jama'a bisa ga yawan jama'ar shekarar 2010 da ƙididdigar gidaje 58,435. Wannan yanki ya kunshi maza 29,742 da kuma mata 28,693.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Bureau, Communications. ""Sefwi Wiawso Is Capital Of Western-North Region" – President Akufo-Addo". presidency.gov.gh (in Turanci). Retrieved 2020-08-25.
- ↑ "NEW DISTRICTS & NOMINATED DCEs" (PDF). ghanadistricts.com. Archived from the original (PDF) on 5 March 2013. Retrieved 22 December 2020.
- ↑ "New Districts & Nominated DCEs" (PDF). ghanadistricts. Archived from the original (PDF) on 5 March 2013.
- ↑ "All Districts". ghanadistricts. Retrieved 8 June 2018.
- ↑ "Districts of Ghana". statoids. Retrieved 8 June 2018.
- ↑ "One person found dead after galamsey pit collapse at Campso - MyJoyOnline.com". www.myjoyonline.com (in Turanci). Retrieved 2021-05-29.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 "Juaboso District Assembly". ghanadistricts.gov.gh. Archived from the original on 1 April 2023. Retrieved 22 December 2020.