Julian Nagelsmann
|
| |||||||||||||||||||||||||||
| Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
| Haihuwa |
Landsberg am Lech (en) | ||||||||||||||||||||||||||
| ƙasa | Jamus | ||||||||||||||||||||||||||
| Harshen uwa | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||
| Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
| Harsuna | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
| Sana'a |
association football coach (en) | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
| Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||
| Tsayi | 189 cm | ||||||||||||||||||||||||||
| IMDb | nm6921083 | ||||||||||||||||||||||||||

Julian Nagelsmann (An haife shi ranar 23 ga watan Yuli, 1987) ƙwararren mai horar da ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda a halin yanzu shine manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus. Ya taba jan ragamar TSG Hoffenheim da RB Leipzig da Bayern Munich a gasar Bundesliga.
Farkon rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife shi a Bavaria, Nagelsmann ya yi ritaya a matsayin ɗan wasan ƙwallon ƙafa yana da shekaru 20 bayan raunin da ya samu. A shekara ta 2010, ya fara aikin horarwa a matsayin kocin matasa a TSG Hoffenheim, inda daga karshe ya horar da kungiyarsu ta farko a shekarar 2015, inda ya kai su matsayi na uku a gasar Bundesliga da gasar cin kofin zakarun Turai. Ya bar Hoffenheim a cikin 2019 kuma an nada shi a kungiyar ta RB Leipzig ta Bundesliga, inda ya kai wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai a 2020.
Bayern Munich ta nada Nagelsmann a shekara ta 2021 kan cinikin rikodi a duniya wanda ya kai Yuro miliyan 25 kwatankwacin fam miliyan 21.7, wanda hakan ya sa ya zama koci mafi tsada. Ya lashe kofin Bundesliga a kakar wasa ta farko, amma an kore shi a matsayin koci daga kungiyar a watan Maris 2023.