Julienne Keutcha
Julienne Keutcha | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kameru, 21 Oktoba 1924 | ||
ƙasa | Kameru | ||
Mutuwa | 2000 | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Jean Keutcha (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Julienne Keutcha (21 Oktoba 1924 - 2000) yar siyasar Kamaru ce. A shekarar 1960 ita ce mace ta farko da aka zaɓa a Majalisar Dokokin ƙasar Faransa ta Kamaru.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Keutcha a cikin shekarar 1924 a ƙauyen Ngwatta kusa da Santchou. [1] Ta kammala karatu daga makarantar kyakkyawa (beauty institute) a Paris, [2] kuma ta zama ma'aikaciyar kula da yara. Ta auri Jean Keutcha, wanda daga baya ya zama minista da jakade. [1]
Ta kasance ‘yar takara a zaɓen ‘yan majalisa na shekarar 1960 kuma ta zama mace ta farko da aka zaɓa a majalisar dokokin ƙasar. Ta kasance a ofishin har zuwa shekara ta 1972. A lokacin zamanta a majalisa ta kasance sakatariyar ofishin kuma ta zauna a kwamitin kula da harkokin waje. [1] Ta kuma zama mamba a ofishin kungiyar ta Kamaru kuma ita ce mace ɗaya tilo a cikin kwamitin a lokacin. [3]
Ta mutu a shekara ta 2000. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 Les 50 femmes des 50 dernières annés (25) KEUTCHA Julienne Ici Cameroon
- ↑ 2.0 2.1 The Founding Mothers Focus International
- ↑ Mark Dike DeLancey, Mark W. Delancey & Rebecca Neh Mbuh (2019) Historical Dictionary of the Republic of Cameroon p291