Ƙaho
Kaho/Hijama wata hanya ce da ake neman lafiya daga cututtuka da suka damu Dan adam. Kaho ya samo asali tun iyaye da kakanni kuma anayin shi musamman a kasar Hausa.
Yadda Ake Kaho
[gyara sashe | gyara masomin]Shi dai kaho ana yinsane a gargajiyance ta hanyar amafani da kahon dabba wanda ka sarrafa, musamman ma kahon kananan dabbobi kamar raguna, awaki da Tumaki. Akan yanka kahon a gogeshi dai-dai yadda zai bada damar kafashi a cikin mutum. Idan za'a yiwa mutum Kaho, wanzami zai dasa kahon a dai dai inda ke da tararren mataccen jini a jikin mutum. A na amfani da aska domin yin tsaga a dai dai wajen kafun a sanya kahon a rufe, sai kuma a sanya baki a saman kahon wanda yakeda dan rami karami, sai wanzami yasa bakinsa akan ramin yayita hurawa yana zuqowa har sai mataccen jinin ya fito duka. A yau, cigaban zamani ya zamanantar da yadda ake kaho sannan an samarda kayan aiki na roba ba tareda anyi amfani da kaho ba, [1]
Amfanin Ƙaho ga Ɗan Adam
[gyara sashe | gyara masomin]Kaho ya kasance hanya mafi sauki wajen yaki da cututtuka wadanda ma ba a san suna wanzuwa a jikin dan adam ba. Binciken likitanci na zamani yan tabbatar da cewa yin kaho kariya ce daga kamuwa da hawan jini ko kuma ciwon da suke da alaka tsarin kwayoyin halitta da ciwukan da suke da alaka da Zuciya. Bugu da kari har matsalolin kwakwalwa za a iya magance su ta hanyar yin kaho.[2]
Asali
[gyara sashe | gyara masomin]Kaho ya samo asali ne tun shekaru dubbai da suka gabata a kasar Sin, inda suke amfani da shi wajen maganin matsalolin jini da ciwon jiki. Ka ga ke nan ba aikin likitancin zamani irin namu ba ne.[3][4][5]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.medicalnewstoday.com/articles/324817
- ↑ https://www.masnad.com.au/hijama-therapy-benefits-traditional-modern-perspectives/#:~:text=Traditionally%2C%20hijama%20treats%20various%20health,and%20boosting%20the%20immune%20system.
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/amsoshin-tambayoyin-daban-daban-tsakanin-ruwan-jikin-mutum-da-jini-wanne-ya-fi-muhimmanci
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/amsoshin-tambayoyin-daban-daban-tsakanin-ruwan-jikin-mutum-da-jini-wanne-ya-fi-muhimmanci
- ↑ https://aminiya.dailytrust.com/amsoshin-tambayoyin-daban-daban-tsakanin-ruwan-jikin-mutum-da-jini-wanne-ya-fi-muhimmanci