Kamfanin zane na "Norman and Dawbarn"
Appearance
Kamfanin zane na "Norman and Dawbarn" | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | architectural firm (en) |
Norman and Dawbarn (mai salo Norman & Dawbarn, kuma daga baya, Norman + Dawbarn) kamfanin zane-zane ne da kere-kere na Biritaniya, wanda aka kafa a cikin 1934.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Graham Dawbarn da Nigel Norman ne suka kafa wannan ma'aikata a cikin shekarar 1934. Norman, Muntz & Dawbarn ne suka gabace shi, wanda suka kafa tare da Alan Muntz.
A cikin shekara ta 2005 Capita Symonds ya mallaki ma'aikatar bayan rushewarta. Ta koma aiki a karkashin kulawar Capita Norman + Dawbarn har zuwa lokacin da sukayi maja da Capita Architecture a 2007, kodayake an ci gaba da amfani da sunan a wasu kasuwannin duniya.
Sanannun ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]- Cibiyar Talabijin ta BBC - An tsara ta 1949, an gina ta 1953 zuwa 1960
- Jami'ar Malta harabar, Msida, Malta - Tsara 1961, gina 1964 zuwa 1970
- Makarantar Budanilkantha, Nepal - Kammala 1973
Sanannun ma'aikata
[gyara sashe | gyara masomin]- Bill Bradfield
- Gertrude Leverkus
- Michael Manser