Karin magana

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Karin magana magana ce ko zance da hausawa kan yi wanda ke dauke da hikima da basira aciki, domin yin hannunka mai sanda da huce takaici akan wani abinda aka yi maka.


Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai:

Farfesa Ɗangambo (1984) da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kaɗan, cikin hikima”.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992) , “Karin Magana Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai faɗi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki”.

Kenan idan aka lura sosai, za a ga cewa ita karin magana, magana ce dunƙulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Amma yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shuɗe, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abinsa. Misali, ana iya yiwa mutumin da bashi da tattali nuni cikin ‘yan kalmomi marasa yawa, kamar a ce da shi, wannan abin da ka ke yi zai hana ka farcen susa. Ko kuma idan ana son yin magana game da wani abu mai amfani da kuma maras amfani. Kamar a ce idan an aikata abin, wani abu maras daɗi zai faru da wanda ya aikata, to ana iya yi masa nuni ta hanyar cewa da shi, wannan abin ba zai haifar maka da ɗa, mai ido ba. Da sauransu.

Kowace ɗaya aka ɗauka daga cikin waɗannan karin magana guda biyu, za a taras cewa maganganu ne dunƙulallu, waɗanda idan aka tashi farfasa su, za su ci guri mai yawa. Amma idan aka faɗe su da baki ko aka rubuta su, za a ji su ko a gan su gajeru, sannan kuma shi wanda ake magana da shi zai iya fahimtar abin da ake nufi. https://rumbunilimi.com.ng

Amfanin Karin Magana[gyara sashe | Gyara masomin]

 1. Taƙaita doguwar magana.
 2. Nuni, gargaɗi, da faɗakarwa cikin nishaɗi, sannan kuma a taƙaice.
 3. Bayyanar da ƙwarewa da fasahar Bahaushe wajen iya magana.
 4. Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana ƙarawa zance kyau da kuma daɗi.

https://rumbunilimi.com.ng

Misalai[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Kowane bakin wuta, da nashi hayaki
 • Komi tsufan zaki, ya fi saurayin kare
 • Komi jarabar bunsuru, ya kiyayi matar kura
 • Komi nisan jifa, Ƙasa zai faɗo
 • Wuta da Aljanna duka na Allah ne. Inji mai sabo
 • Duk wanda ka gani a inuwa, ba ta can faro ba.
 • Idan ka ji wane, ba banza ba.
 • Taya taito, yafi ban cigiya.
 • Rashin jini, rashin tsagawa.
 • Idan kaga ki gudu yaki gudu, sa gudu ne bai zo ba.
 • Da mai rai ake rikicin duniya
 • Aikin banxa antura agwagwa ruwa