Fassara
Fassara ita ce juya ko sauya wata magana daga wani harshe zuwa wani. Wannan magana tana iya zama baka da baka, rubutacciya, daga baka zuwa rubutu, ko kuma daga rubutu zuwa maganar baka. Misali, idan na faɗi magana da Hausa, kamar in ce, “Ado mutumin kirki ne”, sai kai kuma ka juya ta zuwa Turanci ka ce, “Ado is a generous person”. To, fassara ta samu amma ta baka da baka. Ko kuma a rubuta “ ﻫَﺬَﺍﻛِﺘَﺎﺏٌ ”, kai kuma ka juya ta zuwa “wannan littafi ne”. A nan ma an yi fassara amma rubutacciya daga Larabci zuwa Hausa.[1]
Ma’anar Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]Masana sun bata ma’ana ta, fasahar mayar da wani abun da aka faɗa ko aka rubuta daga wani harshe zuwa wani ba tare da canja ma’anarsa ba (Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yaraduwa, 1992; Sani, Muhammad, da Rabeh, 2000).[2]
Rabe-Raben Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]An raba fassara zuwa kala biyu:
1. Fassarar kai tsaye: Fassara ce da mai yinta ya ke fassara abu ba tare da canja tsari, salo, da kuma ma’anar abin ba. A nan ana fassara abin ne yadda yake a wancan harshen. Fassarar da ta shafi addini, wato idan za a fassara littattafan addini, kamar hadisi, ko Ƙur’ani da sauransu, ko kuma za a yi fassara a fagen kimiyya, to ba a canja ma’anar kalmar. Misali, idan za a fassara “ ﺃَﻭَّﻝُ ﻣَﺎ ﻳَﺠِﺐُ ”, sai a ce “farkon abin da ke wajaba”. Wannan salon fassara shi ake kira fassara maras ‘yanci.[3]
2. Fassara mai ‘yanci: Fassara ce da mai yinta ya ke da cikakkiyar dama ta fassara abu a yadda ya fahimce shi, amma ba tare da ya canja manufa ba. Wato ita wannan fassarar ana karanta abin ne sannan a juya shi yadda aka fahimce shi. Ana yin wannan fassara a cikin abubuwan da suka shafi labari, jawabi, wasanni, da sauran makamantansu.
Rukunan Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yaraduwa (1992), sun zayyana abubuwa huɗu a matsayin rukunan fassara kamar haka:
1. Naƙaltar harsuna: Abin da ake nufi a nan shi ne cewa dole ne mai yin fassara ya san harsunan da zai yiwa fassara, sannan kuma ya yi musu kyakkyawar fahimta; wato ya san harshen da aka yi maganar da shi, sannan kuma da wanda zai juya maganar zuwa cikinsa. Misali, wanda zai riƙa yin fassara daga Turanci zuwa Hausa, to dole ya fahimci harshen Hausar da kuma na Turanci, fahimta kuma ta haƙiƙa.
2. Sanin al’adu: Dole ne mai yin fassara ya san al’adun waɗanda zai fassara maganar zuwa harshensu. Misali, idan mai fassara zai yi fassara zuwa harshen Hausa, to dole ya san al’adun Hausa , sani kuma ba na shanu ba.
3. Bincike: Dole ne mai yin fassara ya kasance mai zurfafa bincike a fannonin ilimi dan ya samu isassun kalmomin da za su taimaka masa wajen yin kyakkyawar fassara.
4. Ƙamus: Dole ne mai yin fassara ya mallaki ƙamus na harsunan da ya ke yin fassara a cikinsu.[2]
Matakan Yin Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]1. Karatu: Karatu a nan yana nufin mai yin fassara ya karanta abin da zai fassara, karatu na haƙiƙa. Zai yi kyau mai fassara ya karanta abin da zai fassara, sannan ya sake maimaitawa har sai ya fahimci abin da zai fassara ɗin sosai.
2. Gwaji: Bayan an karanta kuma sai a gwada yin fassarar. Ana iya yin haka ta hanyar yanko wani ɓangare na abin da aka karanta a fassara shi, sannan a yi nazarinsa a ga yadda abin ya ke, abin ya dace ko kuwa.
3. Aiki: Mataki na ƙarshe kuma shi ne a shiga aikin fassarar gadan-gadan.[2]
Abubuwan Lura Wajen Yin Fassara
[gyara sashe | gyara masomin]Yana da matuƙar muhimmanci mai fassara ya kiyaye waɗannan abubuwan:
1. Yin amfani da sassauƙar Hausa. Abu ne mai kyau mai yin fassara ya yi amfani da sassauƙar Hausa wacce za ta yi sauƙin fahimta a wajen mai karatu.
2. Fassarar Kalma da Kalma:
Akwai fuska biyu dangane da wannan gaɓa. An so yin fassarar kalma da kalma ko jimla da jimla a fagen addini. Ba a son yin fassarar kalma da kalma a yanayin fassara labari da makamantansa. Wato kenan, idan za a yi fassarar kai tsaye, to, ana yinta ne ta hanyar kalma da kalma. Idan kuma fassara mai ‘yanci ake yi, to, fassarar kalma da kalma, ko jimla da jimla abar ƙyama ce.
3. Gauraye: Cakuɗa ƙarya da gaskiya a cikin fassara, abu ne da bai dace ba, kar ka aikata!
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B.S.Y. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 3. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.
- ↑ Sani M.A.Z., Muhammad A., da Rabeh B. (200). Exam Focus Hausa Language Don Masu Rubuta Jarabawar WASSCE da SSCE. University Press PLC, Ibadan-Najeriya.