Kate Molale
Kate Molale | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 2 ga Janairu, 1928 |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Mutuwa | 9 Mayu 1980 |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | African National Congress (en) |
Kate Molale OMSS (22 Janairu 1928 - 9 Mayu 1980) ta kasance mai fafutukar siyasa ta Afirka ta Kudu, daga shekarar 1970 zuwa 1975 ta wakilci Kungiyar Mata ta ANC / Sashen Mata a Ƙungiyar Demokradiyyar Mata ta Duniya .
Ta shiga reshen Sophiatown na African National Congress a farkon shekarun 1950. A shekara ta 1954 an zabe ta kujerar sakatariyar reshen Sophiatown ANC . Ta shahara a fafutuka turjiya game da tilasta korar mazaunan Sophiatown. Ta tattara mutane a kan Dokar Ilimi ta Bantu ta 1953, ta shirya majagaba (Masupatsela) don karfafawa makarantar don nuna rashin amincewa da Dokar Ilimi na Bantu.[1][2] A karkashin jagorancinta an sanya yara da yawa da basu karatu a makarantu a Sophiatown, Orlando, Brakpan, Randfontein da Alexandra.[1][1]
Molale ta zamo memba na Hukumar zartarwa ta kasa na Kungiyar Mata ta ANC . Ta kuma kasance sakatariyar kungiyar matasa ta ANC ta Transvaal . [1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 OBITUARY KATE MOLALE Error in Webarchive template: Empty url.
- ↑ "Department of Social Development – Address by the Minister of Social Development, Dr Zola Skweyiya, on the occasion [sic] of the National Launch of the Masupatsela Youth Pioneer Programme, Mbombela Municipality, Mpumalanga Province, 24 October 2008". dsd.gov.za. Retrieved 23 May 2018.