Kudin cizo
Appearance
Kundin cizo, wanda a turance ake kira da Bedbug wasu kananan kwari ne marasa fiffike da suke shan jinin dabbobi da mutane don su rayu.[1]
Gaskiyan Bayani akan Kudin cizo
[gyara sashe | gyara masomin]- Kudin cizo ƙananan kwari ne marasa fuka-fuki waɗanda ke shan jinin dabbobi masu jini.
- Yawancin kwarin suna cin abinci a kan dabbobi ko mutane yayin da suke barci.
- Mafi girman lokacin da suke shan jinin shine tsakanin tsakar dare zuwa 5 na safe.
- Ana iya ganin cizon da sauri amma yana iya ɗaukar kwanaki 14 kafin a iya gani ido.[1]
Inda ake Samunsu
- Matsuguni
- Otal-otal
- Dakunan kwana
- Jirgin ruwa na tafiye-tafiye
- Motoci
- Jiragen kasa[2]
Maganin kudin cizo
[gyara sashe | gyara masomin]Don kawar da Kudin cizo, zaku iya ɗaukar wasu matakai a gida kamar haka:
- Wanke kayan kwanciya, labule, da tufafinku a cikin ruwan zafi kuma a busar dasu.
- Yi amfani da buroshi mai tauri don goge katifu don cire kwari da kyau kafin a kwashe.[2]
- Yin feshin maganin kwari.[2]