Jump to content

Labaran Ayuba Alhassan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
taswiraai nunj da garin kano

Labaran Ayuba Alasan (an haife shi a ranar 16 ga watan Yuni a shekara ta 1977) a kauyen Durum, karamar hukumar Kabo ta jihar Kano. Ɗan siyasa ne. Ya rike matsayin kansila, kuma an zaɓe shi a matsayin dan majalisa na jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Kabo a zaben shekara ta 2011.

Farkon rayuwa Karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Labaran ranar 16 ga watan Yuni, a shekarar 1977 a kauyen Durum, Ƙaramar hukumar Kano ta Jihar Kano a tarayyar Nigeriya. Ya halarci Makarantar Firamare ta Durum a tsakanin shekara ta 1985 zuwa 1991. Bayan haka iyayensa sun sanya shi makarantar Alkur’ani inda ya haddace Alkur’ani mai girma. A tsakanin shekarar 1993 zuwa shekara ta 1996 ya yi karamar Sakandare ta Kabo a Kabo, sannan ya yi babbar sakandare a karamar hukumar Karaye a tsakanin shekaru ta 1996 zuwa 2000.[1]

A kokarinsa na neman karin ilimi, Honorabul Alhassan ya koma makarantar Alkur’ani.

Tsakanin shekarar 2004 - 2006, ya yi aiki a matsayin kansila.

Ya fito Takarar majalisar a jihar kano a shekara ta 2011 kuma aka zaɓe shi a matsayin dan majalisar jiha.[2]

Ya ƙara lashe zaɓen karo na biyu dana uku a shekara ta 2015 da kuma 2019 A halin yanzu yana wa'adi na uku a matsayin dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kabo. kuma shine yake riƙe da mukamin whip na Majalisar Jihar kano.