Lawal Adamu Usman
Lawal Adamu Usman | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Lawal Adamu Usman, wanda aka fi sani da Mr. La, fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne. wanda a halin yanzu shine, ɗan majalissar dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya a majalissar dokokin Najeriya ta 10. Ya zama zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawa bayan zaɓen Najeriya na shekarar ta 2023, inda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP. A fafatawar da yayi, Mista La ya doke abokin takararsa, na jam'iyyar APC mai mulki wato, Muhammad Sani Abdullahi (wanda aka fi sani da Dattijo).[1][2][3][4][5]
Ya fara takarar kujerar majalisar dattawa tun a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2019 a lokacin da ya fito takara a karon farko. Sai dai ya fuskanci adawa mai karfi daga Sanata Uba Sani, wanda a ƙarshe ya yi nasara a zaɓen, shikuma ya fadi,duk da nasarar da Uba Sani ya samu Mr La bai ƙaraya ba inda a shekarar 2023 ya sake tsayawa takara. Mista La ya tsaya tsayin daka kan burinsa na siyasa, ya kuma ci gaba da aiki tukuru domin yi wa al’ummar Kaduna ta tsakiya hidima.[6]
A yayin da ake tunkarar babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023, Mista La ya tsara dabarun yaƙin neman zaɓe, inda ya samu gagarumin goyon baya daga jam'iyyarsa ta PDP, da kuma 'yan mazaɓar sa daga Kaduna ta tsakiya. Jajircewar sa, da kuma alƙawurran da ya ɗauka na magance buƙatun jama’a sun yi tasiri ga al’ummar da suka zaɓe shi, wanda a ƙarshe ya kai shi ga nasara a zaɓen.
Farkon Rayuwarsa da Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mista La kuma ya tashi duka a Kaduna, wato haifaffen jihar Kaduna ne.Ya halarci Makarantar Firamare ta Demonstration Kaduna, daga nan kuma ya wuce Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Gwagwalada. Mista La ya kammala karatunsa na jami'a ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Duk da cewa Mista La ya fuskanci ƙalubalen jayayya a kan iliminsa, tare da zargin cewa bai halarci makarantar firamare, da sakandare ba.[7][8]
Duba Kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Olafusi, Ebunoluwa (28 February 2023). "lawal-usman-beats-el-rufais-ex-chief-of-staff-to-get-kaduna-central-senatorial-seat". The Cable. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ Mustapha, Ibrahim (2 March 2023). "Celebrating Lawal Adamu the senator-elect". Blueprint. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ Lere, Mohammed (10 September 2023). "Tribunal upholds PDP senator's victory in Kaduna". PremiumTimes. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ Sahabi, Ahmad (28 February 2023). "#NigeriaDecides2023: PDP wins ALL Kaduna senatorial seats". The Cable. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ I. Yaba, Mohammed (28 February 2023). "APC Loses All Senatorial Districts To PDP In Kaduna". Dailytrust.ng. Retrieved 16 September 2023.
- ↑ "Kaduna tuition fees hike: PDP's Mr. LA supports students with N30m". Blueprint. 19 May 2021. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ "Kaduna Central senator's academic credentials genuine, NECO, ABU witnesses tell tribunal". Daily Nigeria. 25 June 2023. Retrieved 13 September 2023.
- ↑ Alabi, Kaduna, Abdulganiyu (16 July 2023). "Kaduna Senator denies alleged certificate forgery, threatens to sue media houses". Guardian.ng. Retrieved 13 September 2023.