Lin Bin
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Sin, 1961 (64/65 shekaru) |
| ƙasa | Sin |
| Karatu | |
| Makaranta |
Sun Yat-sen University (en) |
| Sana'a | |
| Sana'a | Entrepreneur da injiniya |
| Employers |
Xiaomi (mul) |
Lin Bin (An haife shi a shekara ta 1961) ya kasance ɗan kasuwa ne na ƙasar Sin, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kuma mataimakin shugaban Xiaomi.[1]
Karatu da Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Lin ya kammala karatu daga sashen rediyo mai amfani da lantarki a Jami'ar Sun Yat-sen. Daga ba ya sami digiri na biyu a fannin kimiyyar kwamfuta daga Jami'ar Drexel.[1][2]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan kammala karatunsa, Lin ya fara aiki a Microsoft, inda ya yi aiki a ɓangaren Internet Explorer.[1] Daga shekara ta 2006 zuwa shekara ta 2010, ya yi aiki a matsayin darektan injiniya a Google kuma ya yi aiki A matsayin Mataimakin Shugaban Cibiyar Nazarin Injiniya ta Google China.[3] A cikin shekarar 2010 Lin ya kafa Xiaomi tare da Lei Jun da wasu mutane biyar, yana aiki a matsayin shugaban kamfanin.[4] Bayan ya sauka daga matsayinsa a shekarar 2019, ya zama mataimakin shugaban kamfanin.[5]
Lin Bin na cikin jerin biloniya da mujallar Forbes ta fitar a shekarar alif 2022, tare da kimanta dukiyarsa: dala biliyan 5.1, hakan ya saka shi a matsayi na 536 cikin mutane mafiya arziki a fadin duniya.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 4 "Lin Bin". Forbes. Retrieved 2022-04-21.
- ↑ Russell Flannery (2015-03-04). "2015 Forbes Billionaires China Shout-Out: Xiaomi's Bin Lin". Forbes. Retrieved 2022-04-21.
- ↑ Shu, Catherine (29 August 2013). "Xiaomi, What Americans Need To Know". TechCrunch. Retrieved 1 December 2023.
- ↑ Clover, Charles (11 November 2014). "Chinese tech: Selling to the next billion". www.ft.com. Retrieved 1 December 2023.
- ↑ Anmol Sachdeva (2019-12-02). "Xiaomi Co-founder Lei Jun Steps Down as China President Amid Leadership Reshuffle". Beebom. Retrieved 2022-04-21.