Lisa Folawiyo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lisa Folawiyo
Rayuwa
Haihuwa 1976 (47/48 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Sana'a
Sana'a Mai tsara tufafi
Kyaututtuka
Lisa Folawiyo - Mai tsara kayan sakawa

Lisa Folawiyo (an haife ta a shekarar 1976). Ƴar Najeriya ce, kuma Ƙwararriyar wacce aka fi sanin ta da haɗa kayan sakawa na masaku, irin kayan Yammacin Afirka tare da dabarun ɗinki na zamani, tare da fifita kayan kwalliyan zamani.[1][2][3]

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Lisa Folawiyo tana da masaniya a fannin shari’a, wacce ta kuma karanta a Jami'ar Legas .[4][5]

Ayyukan ta[gyara sashe | gyara masomin]

Lisa Folawiyo sanye da nata kayan

Lisa Folawiyo tana da dakunan saida tufafi a Najeriya har ma da New York dake kasar Amurka. Shahararrun mutane irin su Issa Rae sun sanya kayanta. Rae ta saka rigar ta a cummerbund ga BET tana gabatar da shirin Girke- girke na Baƙin Fim na Amurka .[6] An kuma baje kolin tarin kayan nata a Amurka, Ingila, Najeriya da Afirka ta Kudu. A shekarar 2012, an nuna ta a Vogue Italia. [7]

Kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

  • 2012: Kyautar Afirka
  • 2014: kyautar daya daga cikin baiwa guda takwas masu fitowa daga WWD Wear ta Mata a Yau
  • 2015: An nuna ta a BOF500

Rayuwar ta[gyara sashe | gyara masomin]

Folawiyo ta yi aure tsawon shekaru 14 da suka wuce, tana da yara biyu. Surukinta (baban mijinta) nutum ne mau tafiyar da harkar masana'antu, mai suna Wahab Iyanda Folawiyo .[8][9][10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

*http://www.lisafolawiyo.com/