Jump to content

Loma (woreda)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Loma

Wuri
Ƴantacciyar ƙasaHabasha
Region of Ethiopia (en) FassaraSouthern Nations, Nationalities, and Peoples' Region (en) Fassara
Zone of Ethiopia (en) FassaraDawro Zone

Loma na daya daga cikin gundumomi a yankin al'ummar Habasha ta kudu maso yammacin kasar Habasha. Daga cikin shiyyar Dawro Loma tana iyaka da kudu da shiyyar Gamo gofa, daga yamma sai Isara, arewa maso yamma da Mareka, daga arewa kuma tayi iyaka da Gena Bosa, daga gabas kuma tana iyaka da shiyyar Wolayita. Gabas da kudancin iyakar Loma na da alamar kogin Omo. Garuruwan Loma sun hada da Loma Bale. Loma wani yanki ne na tsohuwar gundumar Loma Bosa.

Dangane da ƙidayar jama'a ta shekarar 2007 da CSA ta gudanar, wannan yanki tana da jimillar mutane 109,192, daga cikinsu 55,214 maza ne da mata 53,978; 3,999 ko kuma 3.66% na yawan jama'arta mazauna birni ne. Yawancin mazaunan Furotesta ne, tare da 64.35% na yawan jama'a suna ba da rahoton imani, 24.06% suna yin addinin Kiristanci na Orthodox na Habasha, 8.31% sun rungumi Katolika, kuma 2.35% sun yi imani na gargajiya.