Jump to content

Lucie Nizigama

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lucie Nizigama
Rayuwa
Haihuwa Ruyigi Province (en) Fassara, 1 Mayu 1957
ƙasa Burundi
Mutuwa Satumba 2010
Sana'a
Sana'a masana

Lucie Nizigama (1 Mayu 1957 - Satumba 2010) ƙwararriyar mai shari'a ce 'yar kasar Burundi kuma mai fafutukar kare haƙƙin mata. Ta mutu a shekarar 2010.[1]

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nizigama a ranar 1 ga Mayu 1957 a lardin Ruyigi. Bayan rasuwar mahaifinta, mahaifiyarta ta shiga fafatawa da surukanta kuma sun yi doguwar shari'ar kotu don samun damar cin gadon iyalansu.

Mahaifiyar Lucie ta iya saka ta a makaranta. Ta na da wasu 'yan'uwa uku. Ta ci gaba da karatun lauya bayan shekaru, amma dole ne ta katse karatun ta, don ci gaba da karatun a 1998 kuma ta kammala a 2001. Sannan ta yi aiki a matsayin majistare kuma ita ce mace ta farko mai shari'a a lardin Karuzi na karkara. Sannan ta bude kamfanin lauyoyi a shekarar 2002.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Yakin basasar Burundi ya kara wahalhalun da galibin al'ummar kasar ke fuskanta, don haka a shekarar 2004, Nizigama ta rufe ayyukanta, ta kuma dukufa wajen kare mata ta hanyar ba da taimakon shari'a a kungiyar lauyoyin mata ta Burundi (AFJ). Ta kuma kasance mai taka rawa a kungiyar Christian Action for the Abolition of Torture, wadda ta zama shugabar kasa a Burundi.

Ta gudanar da bincike kan cin zarafin mata. Ta yi ƙoƙarin inganta sauye-sauyen dokoki game da yancin mata da kuma biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa, kuma ta shiga cikin daftarin dokar hukumar gaskiya da sulhu ta ƙasarta.

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Ta mutu a watan Satumbar 2010 bayan ta yi fama da rashin lafiya.[2][3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Burundi: Lucie Nizigama est partie. | Les nouvelles du Burundi – Burundi Africa Generation". burundi-agnews.org (in Turanci). Retrieved 2017-11-08.
  2. "Lucie Nizigama: A great loss for the African human rights community". Database of Press Releases related to Africa – APO-Source (in Turanci). 2010-09-22. Retrieved 2017-11-08.
  3. "Décès de Lucie Nizigama, grande militante burundaise des droits humains". Arib. 2010-09-22. Retrieved 2017-11-12.