Luntiang Pilipinas
Luntiang Pilipinas |
---|
Luntiang Pilipinas shiri ne na gandun daji na birni na kasa acikin Philippines, wanda Sanata Loren Legarda ya kafa acikin shekara ta alif dari tara da casa'in da takwas 1998, ya himmatu don habaka kariyar muhalli da wayar da kan jama'a a tsakanin Filipinas.[1][2]
Shiga zaben 2019
[gyara sashe | gyara masomin]Domin ya tsaya takara a jerin jam’iyyu a zaben fidda gwani na jam’iyyar 2019, Luntiang Pilipinas ya mika takardar shaidar tsayawa takara da karbuwa a ranar 16 ga watan Oktoba, shekarar 2018. Kungiyar-jerin jam'iyyar ta zabi Harry Roque, tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, da Ciara Sotto, mawaka da 'yar wsan kwaikwayo. Daga baya, Roque zai janye daga takarar don tsayawa takarar Sanata, kuma Michael Lim Ubac, tsohon dan jarida na jaridar Philippine Daily Inquirer, ya maye gurbinsa. Legarda ta kasance daya daga cikin wadanda aka zaba a jerin jam'iyyar, amma ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar majalisar wakilai a Antique.Luntiang Pilipinas ya samu kuri'u 59,096 ne kawai, wanda ya gaza yawan adadin da ake bukata don samun akalla kujera daya a majalisar wakilai.