Maƙoƙo
Maƙoƙo | |
---|---|
Description (en) | |
Iri |
thyroid gland disease (en) cuta |
Specialty (en) |
endocrinology (en) nuclear medicine (en) |
Medical treatment (en) | |
Magani | L-thyroxine (en) , methimazole (en) , propylthiouracil (en) , thyroglobulin (en) , triiodothyronine (en) da L-thyroxine (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10-CM | E04.9 |
ICD-9-CM | 240.9 |
DiseasesDB | 5332 |
MedlinePlus | 001178 |
eMedicine | 001178 |
MeSH | D006042 |
Disease Ontology ID | DOID:12176 |
Maƙoƙo (Turanci: goitre) kumburi ne a cikin wuya sakamakon girmamar tsokar Tairod (thyroid).[1]. Ana iya alakanta Maƙoƙo da Tairod wanda baya aiki yadda ya kamata[2], inda yawa ko karancin zubar sinadarin Tairod a jiki kan haifarwa[3]
Fiye da kashi 90% na cututtukan na faruwa ne ta rashin sinadarin Aidin[4] Kalmar ta fito ne daga Latin gutturia, ma'ana makogwaro. Yawancin Maƙoƙo ba su da ciwon daji, ko da yake suna iya yin illa.
Alamomin Maƙoƙo
[gyara sashe | gyara masomin]Alamomin Maƙoƙo sun hada da Kullun a gaban wuya, kusa da makogwaro, Jin matsewa a yankin makogwaro, kumburin jijiyar wuya, tari, Wahalar hadiya, Saurin bugun zuciya (tachycardia), zawo. zufa ba tare da motsa jiki ko ƙara yawan zafin jiki ba, da kuma girgiza[3].
Sanadi/Silar Maƙoƙo
[gyara sashe | gyara masomin]A duk duniya, abin da ya fi zama sanadin goiter shine rashin sinadarin Aidin, wanda aka fi gani a ƙasashen da da kyar suke amfani da gishirin mai dauke da sinadarin Aidin. Ana kuma la'akari da ƙarancin sinadarin selenium a matsayin abin taimakawa. A cikin ƙasashen da ke amfani da gishiri mai dauke da siadarin Aidin, Hashimoto's thyroiditis (Maƙoƙon Hashimato) shine yafi kasancewa sanadi[5]. Maƙoƙo kan iya samuwa ta sanadin Gubar sayanaid (Cyanide), wanda ya zama ruwan dare a ƙasashe masu zafi inda mutane ke cin tushen rogo mai arzikin Sayanaid a matsayin babban abinci[6].
Bincike
[gyara sashe | gyara masomin]Ana iya gano cutar Maƙoƙo ta hanyar gwajin aikin Tairod (Thyroid function test), ga wanda dake zargin yana da shi[7].
Nau'ukan
[gyara sashe | gyara masomin]Ana iya rarraba ana iya rarraba Maƙoƙo kashi biyu, ko dai a matsayin Me-kololo nodular ko Me-yaduwa. Maƙoƙo Me-kololo ko dai na kololo ɗaya ne (uninodular) ko na kololo da yawa (multinodular[8]). Maƙoƙo Me-kololo da yawa shine yafi yawa gurin saka rashin lafiya na jijiyar Tairod[9].
wata cuta ce da take fitowa a wuyan mutum, takanyi kumburi sosai.[10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Thyroid Nodules and Swellings". British Thyroid Foundation. 11 September 2019
- ↑ "Goitre - NHS Choices". NHS Choices. 19 October 2017
- ↑ 3.0 3.1 Can AS, Rehman A. Goiter (https://www.ncbi.nlm.nih.gov/books/NBK562161/). [Updated 2021 Aug 30]. In: StatPearls [Internet]. Treasure Island (FL): StatPearls Publishing; 2022 Jan-. Accessed 6/6/2022.
- ↑ Hörmann R (2005). Schilddrüsenkrankheiten Leitfaden für Praxis und Klinik (4., aktualisierte und erw. Aufl ed.). Berlin. pp. 15–37. ISBN 3-936072-27-2.
- ↑ Mitchell RS, Kumar V, Abbas AK, Fausto N (2007). Robbins Basic Pathology (8th ed.). Philadelphia: Saunders. ISBN 978-1-4160-2973-1.
- ↑ "Toxicological Profile For Cyanide" (PDF). Atsdr.cdc.gov. Archived (PDF) from the original on 28 July 2004. Retrieved 16 March 2017
- ↑ Goitre". nhs.uk. 19 October 2017. Retrieved 27 March 2019
- ↑ "Nodular Goiter - an overview | ScienceDirect Topics". www.sciencedirect.com. Retrieved 6 March 2022
- ↑ feingold, K. R.; et al. (2000). "Multinodular Goiter". MDText.com. PMID 25905424
- ↑ Blench, Roger. 2013. Mwaghavul disease names. Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.