Jump to content

Maɗigo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Madigo)
Maɗigo
group of women (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na female human (en) Fassara, homosexual (en) Fassara, LGBTQ woman (en) Fassara da gynephile (en) Fassara
Gajeren suna WLW
Tuta lesbian pride flag (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassara lesbianism
Mastodon instance URL (en) Fassara https://lesbianschool.com
Hannun riga da gay man (en) Fassara, heterosexual male (en) Fassara da heterosexual female (en) Fassara

Yar' Maɗigo itace mace mai Kaunar Jinsi.[1][2] Kalmar Madigo ana kuma Amfani dashi ga mata don bayyana Yanayin jima'insu ko Ɗabi'ar jima'insu ba tare da duba sexual orientation, ko kuma akanyi amfani da sunan amatsayin siffa dan danganta sunayen mata dake da alaƙa da kaunar jinsun mata yan'uwansu ko kaunar jinsi daya.[2][3]

Maɗigo
'Yan Maɗigo

Fara samun sunan "Madigo" Dan babbanta mata masu kaunar jima'in jinsi yafaru ne a lokacin 20th. A dukkanin tarihi, mata basu taba samun iko da yanci ba, kamar maza dan nema yin alaka ta kaunar jinsi ba, kuma basu taba cin karo da tsananin azabtar wa ba kamar yadda akewa maza maso kaunar jinsi ba a wasu alummomin ba. Saidai akan ga cewa harkar madigo harka ce wacce ba za'a iya gaba hada taba da saduwa ba heterosexual koda ko wacce zata yi zata so tasamu jin dadi kamar yadda maza ke ji tare da mata ba. A sakamakon haka, a tarihi kaɗan ne kawai aka iya chiskewa na bayanai akan ya mata masu madigo ke ji. A sanda sexologists na farko-farko a karni na 19th suka fara rarrabawa da bayyana dabi'ar kaunar jinsi, amma haka ya fuskanci rashin nasara sanadiyar karancin ilimi da sanin kaunar jima'in mace, sun raba yan'madigo amatsayin mata waɗanda basu bin nau'intakar jinsi na mace, sannan kuma suka bayyana su amatsayin masu tabin kwakwalwa, saidai wannan bayyanancin ansauya shi a zamanin daya biyo.

Mata dake cikin alakar kaunar jinsi sun maida martani ga irin wannan bayyanawar kodai ta hanyar boyewa rayuwarsu ko kuma ta karbar sunan da aka basu ta hanyar samar da wani al'adar irin wanda yasamu a Turai da Tarayyar Amurka. Bayan Yaƙin Duniya II, gwamnati ta shiga kama mutane masu kaunar jinsi, mata sun tsaranta alakan saduwa da ilimantar da juna. Karin tattalin arziki da yancin kowa da kowa ya haifar masu a hankalin yadda zasu tsara alaka da hada iyali. tare da second wave feminism da kuma karin yawan ilimantar da mata a tarihi da jima'i a karni na 20th, ma'anar yar'madigo ya faɗaɗa, inda ya haifar da mahawarar cewa sha'awar jima'i amatsayin muhimmin abu da za'a duba a ma'anar yar' madigo me nufi. Wasu mata da suka shiga cikin yin aikin jima'in jinsi daya suna ƙinson akirasu da yan' Madigo ko bisexual.

  1. "Lesbian". Oxford Reference. Retrieved December 10, 2018.
  2. 2.0 2.1 Zimmerman, p. 453.
  3. Committee on Lesbian Health Research Priorities; Neuroscience and Behavioral Health Program; Health Sciences Policy Program, Health - Sciences Section - Institute of Medicine (1999). Lesbian Health: Current Assessment and Directions for the Future. National Academies Press. p. 22. ISBN 0309174066. Retrieved October 16, 2013.