Jump to content

Mahamoud Adam Béchir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mahamoud Adam Béchir
Rayuwa
Haihuwa Biltine (en) Fassara, 1965 (58/59 shekaru)
ƙasa Cadi
Karatu
Makaranta Jami'ar Khartoum
Harsuna Larabci
Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya

Mahamoud Adam Béchir (an haife shi a shekara ta 1965) jami'in diflomasiyyar Chadi ne. A baya ya kasance Jakadan Chadi a Amurka daga shekarar 2004 zuwa 2012.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A haife shi a Biltine cikin shekarar 1965, Béchir ya yi karatunsa ne daga ketare. Bayan samun digiri na farko na Kimiyyar haɗa magunguna a Jami'ar Khartoum, Bechir ya koma Chadi inda aka nada shi shugaba a asibitin soji na HMI. Ya ci gaba da karatunsa a Makarantar Postgraduate Naval a Monterey, Kalifoniya, da kuma Cibiyar Hulda da Jama'a da Soja, inda ya kammala a shekarar 1997 tare da digiri na biyu. An karawa Bechir girma zuwa matsayin Laftanar kanar kuma an sauya shi daga HMI zuwa Ma'aikatar Tsaro a matsayin Daraktan Sansanin Soja. Ya kuma halarci Jami'ar Cranfield ta Ingila.

A shekarar 2004 Shugaba Idriss Déby ya nada Bechir a matsayin jakadan Amurka, Canada, Brazil, Argentina da Cuba.

A shekara ta a 2005, ya ziyarci Jami'ar West Virginia .