Malik Fiaz Ahmad Awan
Malik Fiaz Ahmad Awan | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Hafizabad (en) , 6 Satumba 1960 (64 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Jam'iyar siyasa | Pakistan Muslim League (N) (en) |
Malik Fiaz Ahmad Awan ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba na Majalisar Lardin Punjab, daga shekarar 2008 zuwa watan Mayun shekarar 2018. Shi ma masanin noma ne.[1]
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Awan a ranar 6 ga watan Satumbar 1960 a Hafizabad .[2]
Yana da digiri na Bachelor of Arts.[2]
Harkokin siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Awan ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-79 (Gujranwala-III) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1990 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri’u 11,625 inda ya sha kaye a hannun Noor Muhammad ɗan takarar jam’iyyar Islami Jamhoori Ittehad (IJI).[3]
Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-79 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1993 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri’u 5,848 sannan kuma ya sha kaye a hannun Syed Muhammad Arif Hussain dan takarar jam’iyyar Pakistan Muslim League (PML-N).
Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP) daga Mazaɓar PP-105 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002, amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 24,638 ya kuma rasa kujerar a hannun Muzaffar Ali Sheikh, ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (Q) (PML-Q).[4]
An zaɓe shi zuwa Majalisar Lardi na Punjab a matsayin ɗan takarar PPP daga Mazaɓar PP-105 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 . Ya samu ƙuri'u 34,134 sannan ya doke Haji Rai Riasat Ali, ɗan takarar jam'iyyar PML-Q.[5]
An sake zaɓen shi a Majalisar Lardin Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-105 (Hafizabad-I) a babban zaɓen Pakistan na 2013 .[6] Ya samu ƙuri'u 55,021 sannan ya doke ɗan takara mai zaman kansa, Muzaffar Ali Sheikh.[7]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Malik Fiaz Ahmad Awan - Profile, Political Career & Election History". UrduPoint (in Turanci).
- ↑ 2.0 2.1 "Punjab Assembly". www.pap.gov.pk. Archived from the original on 20 June 2017. Retrieved 15 January 2018.
- ↑ "Punjab Assembly election results 1988-97" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 30 August 2017. Retrieved 12 July 2018.
- ↑ "2002 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 January 2018. Retrieved 24 March 2018.
- ↑ "2008 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 5 January 2018. Retrieved 24 March 2018.
- ↑ "List of winners of Punjab Assembly seats". The News (in Turanci). 13 May 2013. Archived from the original on 16 January 2018. Retrieved 18 January 2018.
- ↑ "2013 election result" (PDF). ECP. Archived from the original (PDF) on 26 May 2018. Retrieved 12 July 2018.