man shanuMan shanu wani nau'in mai ne da ake samo shi a jikin shanu ta hanyar tatso shi, man-shanu dai mai ne wanda ake amfani da shi sosai wajen cin abinci kuma man shanu mai ne da ƙamshin shi ya sha ban-ban da sauran Kalolin mai.kuma ana saka shi a abinci kamar miyan kuka, taushe da sauransu. Bayan An fitad da man Shanu daban sannan akan sake dafa Nonon shanun , don maida shi Kindirmo, Sannan akan kaɗa ɗanyan man a ƙara a cikin dafaffan Kindirmo, Wanda Zai kwanta a samansa Kindirmon don Man ya ƙarawa Kindirmon maiko, wannan Man da ake kaɗawa a zuba a Saman Kindirmon Shi ake ƙira Malanko. MALANKO Wani nau'in mai ne Na madarar Shanu, Wanda kuma ake zubawa a Saman Kindirmo, Bayan an fitar da Shi daga jikin ɗanyan Nonon shanu, Sai a sake maida shi cikin Kindirmo Bayan an kammala dafa Nonon shanun don a ƙarawa Kindirmon Maiƙo.