Maria Elizabeth Simbrão de Carvalho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maria Elizabeth Simbrão de Carvalho
ambassador of Angola to Belgium (en) Fassara

ga Afirilu, 2009 - ga Faburairu, 2018 - Georges Rebelo Chicoti (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Angola
Karatu
Makaranta Agostinho Neto University (en) Fassara
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya

Maria Elizabeth Simbrão de Carvalho ita ce jakadiyar Angola a Belgium, Luxembourg da Tarayyar Turai daga shekarun 2009 zuwa 2018.[1] Georges Rebelo Pinto Chikoti ne ya maye gurbin ta.[2]

Simbrão ta yi karatu a Jami'ar Agostinho Neto ta Angola inda ta sami digiri a fannin shari'a. Ta shiga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ne a shekarar 1976, inda ta gudanar da ayyuka da dama, musamman ta zama sakatariyar shugaban ƙasa kan harkokin ƙasashen waje daga shekarun 1986 zuwa 1990. Bayan ta zama mai ba da shawara a ofishin jakadancin Angola da ke Bonn, ta yi aiki a matsayin darekta-janar na harkokin shari'a da na ofishin jakadancin da kara a ma'aikatar harkokin waje daga shekarun 1994 zuwa 1999. Daga nan aka naɗa ta ƙaramar jakadiya a Lisbon inda ta yi aiki har zuwa shekara ta 2007.[3]

An naɗa ta jakadiyar Angola a Belgium, Luxembourg da Tarayyar Turai a watan Afrilun 2009. A watan Janairun 2013, a ranar al'adun Angola ta ƙasa, ta jaddada buƙatar zuba jari a cikin darussan fasaha, da adana gine-ginen tarihi da bincike na al'adu a Angola.[4]

Bayan shekaru tara na hidima, Shugaba João Lourenço ya sauke Simbrão daga ayyukanta na jakadiyar Belgium a cikin watan Fabrairu 2018.[5] An maye gurbin ta da Georges Rebelo Pinto Chikoti wanda ya yi aiki har zuwa Maris 2020.[6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Diplomat in Belgium highlights Angola's contribution to peace". Angola Press. November 14, 2015. Retrieved 10 May 2020.
  2. "Appointment of H.E. Mr Georges Rebelo Pinto Chikoti, as the Head of Mission of the Republic of Angola to the European Union to replace H.E. Ms Maria Elizabeth Augusto Simbrão de Carvalho" (PDF). General Secretariat of the Council. Retrieved 10 May 2020.
  3. "Nova embaixadora na Bélgica apresenta sexta-feira cartas figuradas" (in Portuguese). ANGOP. 22 April 2009. Retrieved 12 May 2020.CS1 maint: unrecognized language (link)
  4. "Angola: Ambassador Elizabeth Simbrão Speaks of Angolan Culture in Belgium". All Africa. 4 February 2013. Retrieved 12 May 2020.
  5. "Angola: President Sacks Ambassadors". All Africa. Retrieved 7 February 2018.
  6. Bultynck, Guy. "You knew him as Ambassador of Angola, come and meet him as the future Secretary General of the ACP, H.E. Dr Georges Rebelo Pinto Chikoti !". CBL ACP. Retrieved 27 February 2020.