Mariam Boni Diallo
Appearance
Mariam Aladji Boni Diallo (an haife ta a shekara ta 1952) 'yar siyasar kasar Benin ce. Ta kasance Ministar Harkokin Wajen kasar Benin daga ranar 10 ga watan Afrilu, shekarar 2006 zuwa ranar 17 ga watan Yuni 2007.[1]
An haife ta a Nikki a shekarar 1952 kuma ta sami ilimi na duniya. [2] Kafin ta zama Ministar Harkokin Waje, Diallo ta kasance Sakatare-Janar na Ma'aikatar Harkokin Waje tun a watan Maris 2004.[1] Ta kasance mai ba da shawara ga Ofishin Jakadancin Benin a Jamus. Ta yi aiki a matsayin mai baiwa shugaba Boni Yayi shawara kan harkokin diflomasiyya. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Le gouvernement du Bénin, formé le 07 avril 2006" Archived 2007-09-29 at the Wayback Machine, Afrique-express.com (in French).
- ↑ 2.0 2.1 Houngnikpo & Decalo 2013, p. 44