Maryam Jibrin Gidado

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Maryam Jibrin Gidado Jarumar ce a Masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood. An santa a shirin fim mai suna Babban Yaro wanda sukai tare da jarumi Adam A Zango.

Farkon rayuwa da Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Maryam a birnin Jos, jihar Plateau, a watan Disamba, 1988.[1][2]

Tayi karatun firamare a Hassan memorial kafin nan, ta ida firamare school a gangare firamare school, sannan tayi makarantar arabiyya Dake bauchi road duka a cikin garin Jos. Tayi Difloma a ɓangaren Kwamfuta. Ta koma bauchi inda tayi Difloma a bangaren kididdiga ta cigaba har zuwa HND, ta dawo Jos a Jami'ar Jos tayi digiri anan, kasancewar ta bafullatana yasa Akai mata auren wuri tayi aure tun tana da shekaru 13/14, inda harta ta haifi diya mace [ana buƙatar hujja].

Sana'ar Fim[gyara sashe | gyara masomin]

Ta shiga harkan fim, bayan ta fara fim ta auri wani mijin biyo bayan mutuwar auren farko.

Maryam ta fara ne da album din Waka na Mahmud nagudu Mai suna (garin so Nisa) daga Nan tayi fim ita da Ali nuhu a garin Jos Mai suna ( ragowar yaki). Daga Nan fito a fina finai da dama a masana'antar fim ta Kannywood

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

  • Kona gari
  • Munafikin mata
  • Ragowar yaki
  • Fulani
  • Babban yaro[3]
  • Bingyal
  • Mukaddari
  • Ragaya
  • wata hudu
  • Nafi haidar
  • Zawarawa
  • Al,ajabi
  • Sultan
  • Basaja
  • Talatu kanwar shedan
  • da sauran su.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://mybiohub.com/2018/01/maryam-gidado-biography.html/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-22. Retrieved 2023-07-22.