Jump to content

Mr442

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mr442
Rayuwa
Haihuwa 1995 (28/29 shekaru)
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Mubarak Abdulkarim Wanda aka fi sani da Mr 442 An haifeshi a cikin garin Zaria jihar Kaduna 13-9-1995.

KARATU[gyara sashe | gyara masomin]

yayi karatun Firamare da sakandiren sa a Cikin garin zaria sannan Ya karanci ilimin halayyar dan adam (Sociology) a jami'ar Amurka ta Addinai a jamhuriyar Benin.

SHAHARA[gyara sashe | gyara masomin]

Yafara Shahara ne lokacin da ya saki wakar sa da yayi akan wani Sanata mai taken Sanatan nan yayi leaking da kuma wacce yayi wa jarumar masana'antar Kannywood Maryam booth Mai taken Zindir. Mr 442 ya cigaba da yin sunane a cikin kasa Najeriya da Nijer bayan cigaba yin wakoki masu jawo cece kuce a cikin Al'umma, inda ake Alakanta wakokin nasa da Wakokin Batsa wanda hakan Ya saba da Al'adar Hausawa.[1] Inda shi kuma yake kare kansa da cewa jama'a ne suke masa fahimtar da ba dai-dai ba, Shi yanayi hakane Domin janyo Hankalin mutane Su fahimci sakon dake cikin Wakokinsa.

Mr442 da Safaa[gyara sashe | gyara masomin]

Haduwar 442 da Safiyya Yusuf Wacce aka fi sani da Safaa Safaa Tayi tasiri matuka Wajen Kara fito da shaharar 442 a idon duniya Bayan Sun saki wakarsu ta farko mai Taken Kwalele tare da Gudunmawar Madox Tbb

WAKOKIN MR 442[gyara sashe | gyara masomin]

Wasu daga cikin wakokin 442

 • Zindir
 • Ajino Moto
 • Bamaji
 • Soro sok
 • Bura uba
 • daka
 • Sai Monday
 • Kwalelenka ft Safaa ft Madox Tbb
 • Mace Tareda morell
 • Dan hisba yayi leaking
 • Bata kwana
 • Sai babanshi ft tapshak
 • Daka
 • Package ft King Sammy
 • Shagali
 • Yin shine
 • Akan shi
 • Yan mata 2020
 • Corona 2020
 • Bamajin magana ft Teeswags
 • Mr442 2-0
 • Zarians
 • Jikinta ft Ovista ft Teeswagsft

Tee R

 • Tabalaga ft Teeswags
 • Siki saka
 • Kanawan mene
 • Dalla Dalla
 • Lokaci
 • Kotu
 • Mace
 • Riga
 • jigida
 • Yaga mehn ft murja
 • Tunkwal ft Safaa ft murja
 • Basu wuta Ft Safaa

Da sauran su

ANKAMA 442 A KASAR NIGER[gyara sashe | gyara masomin]

An kama Mr 442 da Ola of Kano a Jamhuriyar Nijar a lokacin da suke kokarin yin fasfo din kasar da takardun Bogi na Asalin zama Dan kasar nijar. An kama sune a wata cibiyar yin fasfo da ke Maradi ta iyakar Nijar da hukumar kula da shige da fice, the Direction de la Surveillance du Territoire, DST.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]