Jump to content

Muhammad Ajmal Cheema

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammad Ajmal Cheema
Member of the Provincial Assembly of the Punjab (en) Fassara

15 ga Augusta, 2018 -
District: PP-97 Faisalabad-I (en) Fassara
Member of the Provincial Assembly of the Punjab (en) Fassara

15 ga Augusta, 2018 -
District: PP-108 Faisalabad-XII (en) Fassara
Rayuwa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Pakistan Tehreek-e-Insaf (en) Fassara

Muhammad Ajmal Cheema (an haife shi sha’Uku 13 ga watan Janairun shekarar dubu daya da dari Tara da sittin 1960) ɗan siyasan kasar Pakistan ne wanda ya kasance Ministan Lardi na Punjab na Bait-ul-Mal da walwala, a ofis daga sha’uku 13 ga watan Satumban shekarar 2018 zuwa sha’Tara 19 ga watan Yuli 2019. Ya kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab tun Agustan shekarar 2012.

Sana'ar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya shiga kasar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) a shekara ta 2013. Ya tsaya takara a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 a matsayin dan takarar PTI daga PP-51 Faisalabad-I amma Azad Ali Tabassum na Pakistan Muslim League (N) (PML(N)) ya doke shi.

An zaɓe shi zuwa Majalisar Lardi na Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga PP-97 Faisalabad-I a zaɓen lardin Punjab na shekarar 2018 . Ya samu ƙuri'u 42,405 sannan ya doke Ali Afzal Sahi, ɗan takarar jam'iyyar PTI. [1]

Ya shiga PTI ne bayan zaɓen sa.

A ranar 12 ga watan Satumban shekarar 2018, an shigar da shi cikin majalisar ministocin lardin Punjab na babban minista Sardar Usman Buzdar . A ranar 13 ga watan Satumban shekarar 2018, an naɗa shi a matsayin ministan lardin Punjab na Bait-ul-Mal da walwala.

An cire shi daga mukamin ministan lardin Punjab na Baitul Maal da walwalar jama'a a ranar 19 ga Yulin shekarar 2019.

Ana tuhumar sa da yin zina/goyi bayan zinar Baitul Maal guda ɗaya da kuma jindadin jama'a da yara kanana da yake kula da su. [2]

A ranar 21 ga Mayun shekarar 2022, an cire shi daga zama saboda kaɗa ƙuri'ar adawa da manufofin jam'iyya na zaben Babban Ministan Punjab a ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 2022 [3]

Ya tsaya takarar a matsayin dan takarar PML(N) a zaben fidda gwani na watan Yulin 2022, amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 54,266 sannan Ali Afzal Sahi dan takarar jam'iyyar PTI ne ya doke shi. [4]

Ya tsaya takara a matsayin dan takarar jam'iyyar Istehkam-e-Pakistan a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2024 daga PP-98 Faisalabad-I, amma bai sake yin nasara ba a karo na 3. Ya samu ƙuri'u 25,266 sannan Junaid Afzal Sahi, dan takarar jam'iyyar PTI ya doke shi.

  1. "Election Results 2018 - Constituency Details". www.thenews.com.pk (in Turanci). The News. Retrieved 29 July 2018.
  2. "Scandal of underage girls' forced marriages at state-run shelter home surfaced in Lahore". 29 November 2019.
  3. "ECP de-seats 25 dissident PTI MPs who voted for Hamza Shahbaz". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 2022-05-21.
  4. "PP-97 Faisalabad Bye Election 2022 Result Information". www.electionpakistani.com. Retrieved 2023-08-27.