Muhammad Ibrahim (banker)
Muhammad Ibrahim (banker) | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Federation of Malaya (en) , 1960 (63/64 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
John F. Kennedy School of Government (en) Makarantar Kasuwanci ta Harvard. International Islamic University Malaysia (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Ma'aikacin banki |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Muhammad bin Ibrahim shi ne Gwamna na 8 na Babban Bankin Malaysia. Ya hau kujerar Gwamna a ranar 1 May na shekara ta 2016, inda ya gaji Dr. Zeti Akhtar Aziz. Ya gabatar da takardar murabus dinsa a ranar 6 ga watan Yunin shekara ta 2018.
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad ya kammala karatu daga Makarantar Harvard Kennedy daga digirinsa na biyu a fannin Gudanar da Jama'a a shekara ta 1993. Ya halarci Makarantar Gudanarwa ta mako shida a Makarantar Kasuwanci ta Harvard a shekara ta 2010. Ya sami digiri na farko a fannin lissafi daga Jami'ar Malaya, sannan ya yi difloma a fannin Bankin Musulunci da Kudi daga Jami'ar Musulunci ta Duniya da ke Malaysia .
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Muhammad ya shiga Bankin Negara Malaysia a shekarar 1984, sannan kuma aka nada shi Mataimakin Gwamna a watan Yunin shekara ta 2010. Ya zauna a Kwamitin Manufofin Kuɗi na Banki da kuma Kwamitin Tsayayyar Kuɗi.
A duk lokacin da yake aiki ga Babban Bankin Malaysia, ya rike mukamai da yawa a cikin hukumomin gwamnati da kamfanoni da yawa. Ya kasance memba na kwamitin daraktocin PETRONAS tun daga shekara ta 2010, da na Asusun Mayar da fansho na Malasia tun daga shekara ta 2012 Shine shugaban Cibiyar Kudi ta Asiya tun a shekara ta 2016.
A lokacin rikicin kudi na Asiya, ya kuma kasance manajan darakta na Danamodal Nasional Berhad, wata hukumar sake bankada banki.
Muhammad ya sami lambar yabo ta Tarayyar Malaysia ne Panglima Setia Mahkota ta hannun Yang di-Pertuan Agong a shekara ta 2017.
Bayan rugujewar gwamnatin Barisan Nasional (BN) da kafa sabuwar gwamnatin Pakatan Harapan (PH) a ranar 10 ga watan Mayu shekara ta 2018, Muhammad ya yi murabus kusan wata daya bayan haka a ranar 6 ga watan Yuni shekara ta 2018.