Muhammadu Tambari Dan Muhammadu Maiturare
Muhammadu Tambari Dan Muhammadu Maiturare |
---|
Muhammadu Tambari Dan Muhammadu Maiturare (Haihuwa da Rasuwa:1924 – 1931) Zuwa wannan lokacin an samu cigaba ko kuma kasuwar gidajen dake gadan sarautun zuwa gida biyu Gidan Bello da kuma Gidan Atiku (Atikawa) hakan ya cigaba da kasancewa har zuwa lokacin da daular tambari ta fadi. Duba da haka nada Tambari da akayi ya sabawa tsohuwar tsarin sarautar Sokoto. Kuma shine na karshe da yayi mulki a Kabilan Atikawa. An haifi Muhammadu Tambari a Gwadabawa a shekarar ta Alif (1880) daga dangin Abubakar Atiku Dan Shehu Usmanu Bn Fodio. Shekararsa 44 lokacin da aka nada shi sarautar kuma shine babban Dan Muhammadu Maiturare.[1]
Sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]Kafin sarautarsa ya kasance, shine marufan Sokoto, hakan yasa yana cikin wa inda kuma suka ma turawa mubayi’a kuma suka yarda da tsarin su. Bayan mutuwar Maiturare, turawa suka saka hannu wajen zaban Muhammadu Tambari domin biyayya da yake musu, hakan ya bashi damar zama halifa.[1]
Sauke shi a karaga
[gyara sashe | gyara masomin]An kuma ruwaito cewa Backwell, wani baturen mulkin mallaka ya roki Gwamnan shugaban turawan mulkin mallaka daya sauke tambari a matsayin Kalifa. Gwamna ya nada kwamiti na mutum daya domin binciken laifin da ake tuhumar Tambari dashi, inda daga bisani rahoton binciken ya nuna cewa lallai Kalifa Tambari ya aikata laifin da ake tuhumar shi da ita, kuma rahotan ya kara da cewa lallai ya kamata a cige Kalifa Tambari daga Kalifancinsa. Ganin hakane yasa aka ba Kalifa Tambari shawarar ya baida sandan khalifancinsa da kansa domin gujewa wulakanci. Inda ko hakan akayi ya bada mulkin ga Waziri a ranar 15th January inda Gwamnan turawan mallaka ya amshi ajiye mulkinsa da yayi.[1]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Bobboyi, H., Yakubu, Mahmud.(2006). The Sokoto Caliphate: history and legacies, 1804-2004, 1st Ed. Kaduna, Nigeria:Arewa House. ISBN 978-135-166-7
- Hamman, Mahmoud, 1950- (2007). The Middle Benue region and the Sokoto Jihad, 1812-1869 : the impact of the establishment of the Emirate of Muri. Kaduna: Arewa House, Ahmadu Bello University. ISBN 978-125-085-2. OCLC 238787986.
- Usman Muhammad Bugaje. The Tradition of Tajdeed in West Africa: An Overview International Seminar on Intellectual Tradition in the Sokoto Caliphate & Borno. Center for Islamic Studies, University of Sokoto (June 1987)
- Hugh A.S. Johnston . Fulani Empire of Sokoto. Oxford: 1967. ISBN 0-19-215428-1.
- S. J. Hogben and A. H. M. Kirk-Greene, The Emirates of Northern Nigeria, Oxford: 19
- Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.