Jump to content

Mukhtar Atiku Kurawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mukhtar Atiku Kurawa
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 28 ga Augusta, 1970 (54 shekaru)
Sana'a
Sana'a Malami

Mukhtar Atiku Kurawa farfesa ne a fannin ilimin Inorganic Chemistry, masanin ilmin, mai gudanarwa, kuma tsohon Rector watau shugaban makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Shine shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano watau Vice-chancellor.

An haifi Mukhtar a ranar 28 ga watan Agusta shekara ta, 1970, a unguwar Kurawa, da ke cikin ƙaramar hukumar Kano, ta jihar Kano. Ya sami PhD a Kimiyyar Inorganic Chemistry a Jami'ar Bristol, United Kingdom U. K a shekara ta, 2005.

Kurawa ya koyar a tsangayar Kimiyya ta Jami'ar Bayero ta Kano, sashen ilmin sunadarai har zuwa lokacin da ya zama Farfesan ilimin Kimiyyar Inorganic Chemistry, a shekarar, 2015.

https://dailytrust.com/prof-kurawa-assumes-duty-as-new-vc-of-yumsuk.