Jump to content

Munir Danagundi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Munir Danagundi (an haife shi a ranar 30 ga watan Afrilu 1962) ɗan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Kumbutso. Ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso a farkon shekarun 2000. [1] Ya fara zama ɗan majalisar wakilai a shekarar 2011 zuwa 2015 kuma ya yi aiki har zuwa shekara ta 2023 tare da sake zaɓensa sau biyu. [2]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

Munir ya sami shaidar kammala karatunsa na farko a shekara ta 1978. [1]

Munir ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin majalisar kan kwalejojin aikin gona da cibiyoyi bayan zaɓensa a shekarar 2019 har zuwa 2023. [3] [4] [5]

Ya fara wakilcin mazaɓar Kumbutso a shekarar 2011 a majalisar wakilai ta tarayya. An sake zaɓen sa a karo na biyu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a shekarar 2015. [1]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Hon. Munir Danagundi biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2024-12-11.
  2. "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
  3. Jeremiah, Urowayino (2021-03-24). "Food security: Rep urges FG to address desert encroachment". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-11.
  4. "Reps Urge Minister Of Agriculture To Make Inputs Affordable To Farmers – Independent Newspaper Nigeria" (in Turanci). 2022-11-05. Retrieved 2024-12-11.
  5. "Rep charges agric council to work harder for Act's benefits - Daily Trust" (in Turanci). 2021-11-07. Retrieved 2024-12-11.