Nadia Bakhurji
Nadia Bakhurji | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Saudi Arebiya |
Harshen uwa | Larabci |
Karatu | |
Makaranta | King Faisal University (en) |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | injiniya da Masanin gine-gine da zane |
Nadia H. Bakhurji yar kasar Saudiyya ce kuma yar kasuwa ce.
Sana'a da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]
Bakhurji ta sami BSC a fannin gine-ginen cikin gida daga Jami'ar King Faisal a 1989. Ta kafa kamfanin Riwaq of the Kingdom Est (ROK).
Bakhurji ta zama mamban kwamitin kafa kungiyar mata ta Larabawa a shekarar 2000. Ta zama macen a Saudiyya ta farko da ta yi rajista a matsayin 'yar takara a zaben karamar hukumar Riyadh, a shekara ta 2004, wanda daga baya "hukuman Saudiyya suka soke shi" lokacin da aka haramta zaben mata a Saudiyya.
A shekara ta 2005, ta zama mace ta farko da ta zama mamba a hukumar Injiniya ta Saudiyya. An karɓe ta a cikin lambar yabo na Shugabannin Mata na Gabas ta Tsakiya na 11 a cikin shekara 2012.
A cikin shekara 2007, an kafa Nadia Bakhurji a matsayin mai Gina gine da tsara guri a cikin Riyadh.
Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]
Bakhurji itace babba a cikin 'yan'uwa 7.