Nansana
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Uganda | |||
Region of Uganda (en) ![]() | Central Region (en) ![]() | |||
District of Uganda (en) ![]() | Wakiso District (en) ![]() | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 365,857 (2014) | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC+03:00 (en) ![]() |
Nansana birni ne, da ke a lardin Tsakiya, a ƙasar Uganda. Tana cikin Gundumar Wakiso kuma tana daga cikin kananan hukumomi biyar a cikin gundumar. [1]
Nansana tana kan babbar hanyar mota tsakanin Kampala da Hoima, hanyar Kampala-Hoima. Garin yana kusan kilomita 12 (mil 7), ta hanya, arewa maso yamma na Kampala, babban birnin Uganda kuma birni mafi girma. Wannan kusan kilomita 8 (mil 5), ta hanya, kudu da Wakiso, wurin da hedkwatar gundumar take.
Yawan mutane[gyara sashe | Gyara masomin]
A shekarar 2002, kidayar jama'ar kasar ta sanya mutanen Nansana 62,044. A shekarar 2010, Ofishin Kididdiga na Uganda (UBOS) ya kiyasta yawan mutanen garin 86,200. A cikin shekarar 2011, UBOS sun kiyasta yawan mutanen tsakiyar shekara 89,900. A shekarar 2014, alkaluman yawan jama'a na kasa sun sanya mutane 365,124.