Nawal al-Hawsawi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nawal al-Hawsawi
Rayuwa
ƙasa Saudi Arebiya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Nawal al-Hausawiyya matukiyar jirgin sama ce 'yar kasar Saudiyya.

Wannan ba kasafai aka saba gani ba a kasar ta Saudiyya mai matsanancin riko da addinin Musulunci. Nawal wadda Bahaushiya ce haifaffiyar kasar Saudiyya ta zama zakarar gwajin dafi a kasar inda ta zama mace mai tuka jirgin sama. Alhausawiyya kuma ta na yin fafutika wajen kwato 'yancin matan kasar Saudi Arebiya musamman a fagen maganar wariyar launin fata. Alhausawiyya bakar fata kuma Bahaushiya haifaffiyar birnin Makkah ta auri farar fata baturen kasar Amurika. Ta karya dadaddiyar al'adar kasar ta wadda musulma yar kasar dole sai dai ta auri musulmi mafiyawanci ma farar fata na akasarin yan kasar. Tana da izinin tukin jirgin kasuwanci kuma tana bayar da shawara game da larurar da ta shafi tunani da matsalolin auratayya, wannan kuma abu ne mai kamar wuya ga mata 'yan kasar ta Saudiyya.