Nuhu Abdulqadir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Nuhu Abdulqadir (Kauran Katsina), An haife shi a alif 1947 a karamar hukumar Rimi, Jihar Katsina, Najeriya. An naɗa shi matsayin Kauran Katsina a ranar 17 ga watan Decemban 1982 - sannan daga bisani ya zamo shugaban masu nada sarakuna a birnin Katsina kuma shine wakilin yankin gundumar Rimi.[1]

Kuruciya da Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a 1947 a karamar hukumar Rimi, Katsina. Ya fara karatunsa na firamare a Rafindadi Primary School, ya halarci makarantar Katsina Provincial School don karatunsa na sakandare tsakanin Junairun 1962 zuwa 1966.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Ibrahim, Lawal; Kwaru, Mustapha (March 10, 2008). "Nigeria: Kingmakers Choose Katsina Emir Tomorrow". allAfrica. Retrieved May 30, 2022.