Jump to content

Nusaiba Shuaibu Ahmad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Nusaiba Shuaibu Ahmad (An haifi Nusaiba a shekara ta dubu biyu 2000 a jahar Kano) kuma tana da miji. Itace gwarzuwar musabaƙar Alƙur'ani da akayi a shekarar 2021 wanda aka yi a garin Kano.

Gwarzuwar musabaƙar shekara ta 2021 ta haddace Ƙur'ani tun tana 'yar shekara 15 bayan ta fara haddar littafin mai tsarki tana 'yar 11 zuwa 12, kamar yadda ta shaida wa BBC.[1]

Ta kammala sakandare, inda yanzu haka take zuwa jami'a.

Nusaiba Shuaibu Ahmad ta fara shiga gasar karatu wato musabaƙa a shekarar 2017, Daga cikin nasarorin da ta samu, ta taɓa zama gwarzuwar musabaƙa wadda cibiyar Alfijir ke shiryawa a Kano, Kazalika ta taba zuwa ta biyar a musabaƙar ƙasa, wadda aka gudanar a Jihar Katsina, Suratul Jinn - sura ta 72 - ita ce ta fi bai wa makaranciyar wahala a loƙacin da take hadda. "Saboda tana da ayoyi masu kama da juna," in ji ta.

  1. BBC Hausa. "Gwarzuwar Gasar al-Qurani 2021". Retrieved 28 March 2021.