Obadiah Mailafia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Obadiah Mailafia (an haifeshi ranar 24 ga watan Disamba, 1956 - ya rasu a 19 ga satumba 2021), ya kasance masanin ilimin tattalin arziki ne na kasar Najeriya.

Tarihi rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a garin Randa a Karamar hukumar Singa a Jahar Kaduna dake Najeriya, mahaifinshi Baba Mailafia Gambo Galadima ya kasance mai wa'azi a Evangelist Reformed Church of Central Nigeria RCCG Mailafia an haifeshi kuma anyi renin sa a a cikin wannan cocin ta mahaifinsa yake, Daga baya iyayensa suka tashi daga Randan zuwa Murya, Lafia a Jahar Nasarawa inda ya girma. [1]

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Mailafia ya fara karatun shi a Musha Sudan United Mission School daga shekarar 1964-1969 daga nan ya tafi Mada Hills Secondary School,Akwanga daga 1970-1974, yaci gasar kwamishinan ilimi sakamakomn kwazonsa, ya hallaci makarantar BAsic Studies SBS a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a 1978 daga 1974-1975. Daga baya ya kammala jami'ar da Digiri Bsc. Honours Social Sciences, ya samu digirinsa na biyu Msc. daga jami'ar. Ya cike tallafin karatu na gwamnatin faransa a faransar, inda ya sami shaida ta satificate kan yaren Faransanci da wayewa daga jami'ar Clemont Ferrand a 1985, A 1985 din samu shaidar Diplome (M.Phil) a a International Economics daga Institut International d'Administration Public.[2]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Mailfia ya fara aiki da koyarwar darasin Government da Economics a Akonko AngalicanGrammar School,dake Arigidi-ikare a jahar Ondo Najeriya, daga 1978-1978 wanda na daga cikin aikinsa na bautar kasa bayan kammala digirin sa a jami'ar Ahmadu Bello dake zariya, daga nan ya dawo jami'ar ya fara aiki a Faculty of Arts and Social Sciences daga 1980-198,Lokacin da yake a jami'ar yana koyar da masu karatun digirin farko ne kuma mataimaki a wajen bincike daga Professor.Ibrahim Gambari, wanda daga baya ya zama ministan harkokin kasashen waje kuma mai bada shawara a majalissar dinki duniya a kan harkokin siyasa. [3] daga 1982-1989, Mailafiya

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Mai lafiya ya ne mi takarar shugabanci kasar NAjeriya a shekara ta 2019 karkashi jami'iyyar African Democratic Congress ADC [4]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Mailafiya ya rasu sakamakon annobar korona a shekarar 2021 a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Abuja a Najeriya. [5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kumm, (Hermann) Karl Wilhelm (1874-1930) and Lucy Evangeline [Guinness] (1865-1906) - History of Missiology". Bu.edu. Retrieved 2 March 2019
  2. "Obadiah Mailafia". Blerf.org. 13 March 2017. Retrieved 26 February 2019.
  3. "African Development Bank - Building today, a better Africa tomorrow". African Development Bank. Retrieved 2 March 2019
  4. "Buhari has abandoned talks with Niger Delta leaders". Puchng.com. 13 September 2018. Retrieved 2 March 2019
  5. "Buhari has abandoned talks with Niger Delta leaders". Puchng.com. 13 September 2018. Retrieved 2 March 2019