Ouagadougou

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Hoton Ougadougou.

Ouagadougou (lafazi: /wagadugu/) birni ce, da ke a yankin Tsakiya, a ƙasar Burkina Faso. Ita cne babban birnin ƙasar Burkina Faso kuma da babban birnin yankin Tsakiya. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2015, jimilar mutane fiye da miliyan biyu da dubu dari biyar. An gina birnin Ouagadougou a karni na sha ɗaya bayan haifuwan annabi Issa.