Owunari Georgewill

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Owunari Georgewill
Rayuwa
Haihuwa 15 Mayu 1965 (58 shekaru)
Sana'a
Sana'a Malami

Owunari Abraham Georgewill (an haife shi a ranar 15 ga watan Mayu 1965 [1] ) farfesa ne a fannin harhaɗa magunguna ɗan Najeriya kuma babban mataimakin shugaban jami'ar Fatakwal na 9th. [2][3]

Rayuwar farko da asali[gyara sashe | gyara masomin]

Owunari ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1976 a makarantar Bishop Crowther Memorial, Abonnema. Ya rubuta jarabawar matakin O’Level a makarantar Nyemoni Grammar School, Abonnema a shekarar 1981 sannan a shekarar 1987 ya kammala karatunsa na jami’ar Fatakwal inda ya karanta ilimin haɗa magunguna sannan kuma ya yi digirinsa na biyu a makarantar.[1][4] He holds a bachelor of surgery and a Doctorate of Medicine in Pharmacology and Toxicology.[5] Ya yi digirin farko na tiyata da digirin digirgir a fannin likitanci da magunguna.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Owunari Georgewill ya fara koyar ne a matsayin malami na 2 a sashin ilimin haɗa magunguna na Jami'ar Fatakwal sannan ya zama shugaban tsangayar ilimin likitanci a shekarar 2010. Ya ci gaba kuma an ba shi mukamin Farfesa a fannin harhaɗa magunguna a ranar 4 ga watan Mayu, 2010, yana da shekaru 44. A 2012, an zaɓe shi mataimakin provost na Makarantar Kiwon Lafiya ta Jami'ar Fatakwal kuma a cikin shekarar 2013, an zaɓe shi a cikin Majalisar Gudanar da Jami'ar a matsayin wakili. A ranar 2 ga watan Yuli 2021, majalisar gudanarwar makarantar ta sanar da shi a matsayin mataimakin shugaban jami'a na 9 bayan tantance shi da wasu masu nema goma sha ɗaya.[6][7][2]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Owunari Georgewill ya auri Udeme Owunari Georgewill wacce associate farfesa ce kuma suna da ‘ya’ya huɗu da jika.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Meet Owunari Abraham Georgewill, UniPort 9th Vice Chancellor". www.uniport.edu.ng. Retrieved 13 July 2022.
  2. 2.0 2.1 Chinedu, Clement (2 July 2021). "University of Port Harcourt gets new Vice Chancellor". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 13 July 2022.
  3. https://independent.ng/uniport-alumni-felicitate-with-georgewill-as-9th-vc/
  4. "UNIPORT Alumni Felicitate With Georgewill As 9th VC". Independent Newspaper Nigeria (in Turanci). 6 July 2021. Retrieved 13 July 2022.
  5. "Georgewill's rich experience, unique credentials to lead UNIPORT". News Express Nigeria Website (in Turanci). Retrieved 13 July 2022.
  6. "Georgewill Assumes Office As UniPort 9th VC As Okodudu Bows Out, Relives Experience". www.uniport.edu.ng. Retrieved 13 July 2022.
  7. "UNIPORT governing council appoints VC". Punch Newspapers (in Turanci). 3 July 2021. Retrieved 13 July 2022.