Party for People Dignity

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Party for People Dignity
jam'iyyar siyasa
Bayanai
Farawa 1995
Ƙasa Nijar

Party for People Dignity ( French: Parti pour la Dignité du Peuple , PDP-Daraja) jam'iyyar siyasa ce a Nijar.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa jam'iyyar ne a ranar 2 ga Afrilun shekarar 1995. A zaɓen 'yan majalisar dokoki na shekara ta 1996, wanda manyan jam'iyyun adawa takwas suka ƙauracewa zaɓen, jam'iyyar ta samu kashi 1.4% na ƙuri'un da aka kaɗa, inda jam'iyyar ta lashe kujeru uku daga cikin kujeru 83 na majalisar dokokin ƙasar. [1] Zaɓen shekarata 1999 jam'iyyar tasa an rage yawan ƙuri’unta zuwa kashi 0.1 cikin 100 kawai, wanda ya sa jam'iyyar ta rasa dukkan kujeru uku. Sakamakon makamancin haka a zaɓen shekarar 2004 ya sa jam’iyyar ta ci gaba da zama ba tare da wakilcin ‘yan majalisa ba.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Elections in Niger African Elections database