Placide Nyangala (an haife shi a ranar 30 ga watan Disamba 1967) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Gabon. Bayan Gabon, ya taka leda a ƙasashen; Faransa, Austria da Saudi Arabia. [1] Ya buga wasanni biyu ga kungiyar kwallon kafa ta Gabon a shekarar 1994.[2][3] An kuma saka shi cikin tawagar Gabon a gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 1994.[4][5]