Jump to content

Proscovia Margaret Njuki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Proscovia Margaret Njuki
Rayuwa
Haihuwa 25 ga Yuni, 1951 (73 shekaru)
Mazauni Kampala
Karatu
Makaranta Makarantar Sakandare ta Gayaza
Jami'ar Nairobi
Sana'a
Sana'a injiniyan lantarki, civil servant (en) Fassara da scientist (en) Fassara

Proscovia Margaret Njuki injiniyar lantarki ce kuma ma'aikaciyar gwamnati. Daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2016, tayi aiki a matsayin shugabar hukumar gudanarwar Kamfanin Lantarki na Uganda Electricity Generation Company Limited (UEGCL).[1] Ta maye gurɓin Stephen Isabalija, wanda aka nada babban sakatare a ma'aikatar makamashi da ma'adinai ta Uganda.[2]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife ta a ranar 25 ga watan Yuni 1951 'ya ce ga Reverend da Mrs. Benoni Kaggwa-Lwanga. Ta halarci makarantar sakandare ta Gayaza don karatunta na O-Level da A-Level. Ta yi karatu a Jami'ar Nairobi, inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin injiniyanci na lantarki a shekarar 1974, mace ta farko 'yar Uganda da ta kammala digiri a matsayin injiniya.[3]

Bayan kammala karatunta a Nairobi, ta koma Uganda ta fara aikin injiniyanci na sadarwa a gidan talabijin na ƙasa na lokacin, Uganda Television (UTV). Ta tashi cikin matsayi kuma a cikin shekarar 1994, an naɗa ta shugabar sabis na injiniyanci na UTV. A shekara ta 1995, an nada ta Kwamishina na UTV.[3] Kafin ta zama shugabar hukumar ta UEGCL, ta yi aiki a matsayin mamba a wannan hukumar, ƙarƙashin jagorancin Dr. Stephen Isabalija.[2][4]

Sauran nauye-nauye

[gyara sashe | gyara masomin]

Ita ce wacce ta kafa kungiyar Injiniyoyin Mata, Fasaha da Masana Kimiyya a Uganda, tun a shekarar 1989. Har ila yau, mamba ce a Cibiyar Injiniyoyi masu ƙwarewa a Uganda kuma ta yi aiki a majalisar zartarwa daga shekarun 1990 har zuwa 1993.[3]

A shekarar 1977 ta auri Samwiri HK Nnjuki kuma tare su ne iyayen 'ya'ya mata biyu da namiji ɗaya.[3]

  • Irene Muloni
  • Monica Azuba Ntege
  • Miriam Muwanga
  1. Muhame, Giles (24 November 2016). "Eng Njuki Appointed UEGCL Board Chairperson". Kampala: Chimpreports Uganda. Retrieved 21 June 2017.
  2. 2.0 2.1 UEGCL (2 February 2017). "Dr. Stephen Robert Isabalija handed over to Eng. Proscovia Margaret Njuki, the Chairperson ship of UEGCL". Kampala: Uganda Electricity Generation Company Limited (UEGCL). Archived from the original on 9 November 2017. Retrieved 21 June 2017.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Elizabeth Sleeman (2002). The International Who's Who of Women 2002: The Biography of Proscovia Margaret Njuki. Psychology Press. p. 408. ISBN 9781857431223. Retrieved 21 June 2017.
  4. "Electricity Generation Company UEGCL sees rare profits in 2015". The Independent (Uganda). Kampala. 26 September 2016. Retrieved 21 June 2017.