Ramata Ly-Bakayoko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ramata Ly-Bakayoko
Rayuwa
Haihuwa Abidjan, 29 ga Yuni, 1955 (68 shekaru)
ƙasa Ivory Coast
Karatu
Makaranta Paris Diderot University (en) Fassara
Paris Descartes University (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Malami
Imani
Jam'iyar siyasa Rally of the Republicans (en) Fassara

Ramata Ly-Bakayoko (an haife shi 29 Yuni 1955)[1] Malamar ilimi ce ta ƙasar Ivory Coast kuma jami'iyyar gwamnati ce. Ta yi aiki a matsayin ministar ilimi mai zurfi da bincike na kimiyya ta Ivory Coast daga shekarun 2016 zuwa 2018. An naɗa ta Ministar Mata, Iyali, da Yara a cikin shekarar 2018. An naɗa ta mataimakiyar dindindin ta Cote d'Ivoire zuwa UNESCO tare da zama a Paris a ranar 8 ga watan Satumba, 2021.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Ly-Bakayoko a Abidjan, Ivory Coast, a shekara ta 1955.[1][2] Ta sami digiri a aikin tiyatar hakori daga Jami'ar Paris Diderot a shekarar 1980 da kuma ilimin hakori daga Jami'ar Descartes na Paris a shekarar 1985.[2]

Ly-Bakayoko farfesa ce a fannin likitan hakora na yara.[3] Ta shugabanci sashin kula da ilimin hakora na yara a Jami'ar Cocody (yanzu Jami'ar Félix Houphouët-Boigny) a Abidjan, daga baya ta zama mataimakiyar shugabar tsangayar ilimin hakora, sannan ta zama mataimakiyar shugabar jami'a.[2] Daga shekarun 2012 zuwa 2016, Ly-Bakayoko ta kasance shugaba mace ta farko ta Jami'ar Félix Houphouët-Boigny. A matsayinta na shugaba, ta haɓaka Cibiyar Kimiyya da Ƙirƙira a Bingerville, gida ga shirin Cutar Epidemiology na Yammacin Afirka (WAVE).

Ly-Bakayoko ta yi aiki a matsayin Ministan Ilimi mai zurfi da Bincike na Kimiyya daga shekarun 2016 zuwa 2018, ta gaji Gnamien Konan. Ita ce mace ta farko da ta rike wannan matsayi. A cikin shekarar 2018, an naɗa ta Ministar Mata, Iyali, da Yara.[4]

Kyaututtuka da karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 2018, Ly-Bakayoko ta zama 'yar ƙasar Ivory Coast ta farko na Faransa Académie des sciences d'outre-mer. A cikin shekarar 2019, an ba ta digirin girmamawa daga Jami'ar Franche-Comté ta Faransa.[2][5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Douce, Sophie (2017-12-20). "Q&R : La Côte d'Ivoire en première ligne sur le climat". SciDev.net (in Faransanci). Retrieved 2020-02-09.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "L'université de Franche-Comté décerne le titre de Docteur Honoris Causa au Pr Ramata Bakayoko-Ly". maCommune.info (in Faransanci). 2019-12-18. Retrieved 2020-02-10.
  3. "Ramata Ly-Bakayoko, première Ivoirienne à l'Académie des sciences d'outre-mer de Paris". Le Monde (in Faransanci). 2019-03-08. Retrieved 2020-02-10.
  4. Ouattara, Lacinan (2019). "Côte d'Ivoire : Un nouveau Gouvernement avec 42 ministres et 7 Secrétariats d'Etat". RTI (in Faransanci). Archived from the original on 2019-10-16. Retrieved 2020-02-15.
  5. "Pr Bakayoko-Ly Ramata fait Docteur Honoris Causa de l'université Franche-Comté de France". Agence Ivorienne de Presse (in Faransanci). 2019-12-18. Archived from the original on 2020-02-15. Retrieved 2020-02-10.