Ri Un-ju (an haife ta a ranar 25 ga ga Oktoban shekarar 1983) ƴar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Koriya ta Arewa wacce ke taka leda a matsayin mai tsaron gida. Ita memba ce a Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Koriya ta Arewa . Ta kasance ɗaya daga cikin tawagar a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta shekarar 2003. [1]