Jump to content

Ruzizi Plain

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ruzizi Plain
General information
Labarin ƙasa
Map
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa 3°12′29″S 29°12′37″E / 3.20819°S 29.21028°E / -3.20819; 29.21028
Kasa Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Territory South Kivu (en) Fassara

Filin Ruzizi (Faransanci: Plaine de la Ruzizi) wani kwari ne da ke tsakanin sarkar dutsen Mitumba da kogin Ruzizi. Yana nan ne a matsayin iyakar kasa, wanda ke raba Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC) daga Burundi da Rwanda a daya bangaren. Filin Ruzizi wani yanki ne na babban yankin yammacin Rift Valley, wanda ya mamaye kasashen Afirka da dama. Kogin Ruzizi ne ya ratsa shi, wanda ke kwarara daga tafkin Kivu ta fili zuwa tafkin Tanganyika.