Sa'idu Faru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sa'idu Faru
Rayuwa
Haihuwa 1932 (91/92 shekaru)
Karatu
Harsuna Hausa
Sana'a
Sana'a mawaƙi da maiwaƙe

Sa'idu Faru (1932-) An haifi Sa'idu Faru a garin Faru ta cikin kasar Maradun, Ƙaramar Talatar Mafara a wajajen shekara ta 1932. Sunan mahaifin Sa'idu Faru shi ne makada Abubakar dan Abdu, shi kuwa makaɗa Abdu, Alu mai Kurya ya haife shi. Ita kuwa mahaifiyar Sa'idu Faru mutuniyar Banga ta cikin kasar Kaura-Namoda ce.

Kuruciya: Sa'idu Faru ya yi yawancin kuruciyarsa ce a garin Banga ta Kaura-Namoda inda aka haifi uwarsa, amma kafin ya girma sai ya koma wurin tshohonsa makada Abubakar a Faru.Makaɗa Sa'idu bai samu ilimin Muhammadiya da yawa ba, sai dai an sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga Alkur'ani mai tsarki.

Fara waka: Makada Sa'idu Faru ya koyi waka wurin mahaifinsa makada Abubakar. Tun Sa'idu Faru yana da shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gar-gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha shida, ya soma karbi, a wannan lokaci ne kuma aka hada su tare da kanensa Mu'azu wanda shi ne Dangaladimansa. Baya ga tsohonsa makada Abubakar, Sa'idu Faru bai koyi kida ga koewane makadi ba, dukkan salo iri-iri da yake sakawa a wakokinsa tushensu mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane fasalin waka. Da Sa'idu Faru ya samu cin gashin kansa, ya fara da wata waka mai dadin gaske, kunshe da tarin hikimomi. Ga kadan daga cikinta:

  • Bi da maza Dan Jodi na Iro, Iro magajion Shehu da Bello.
  • Hasken hitila ba dai da wata ba,
  • Tauraro haskenka subahin,
  • Dawaya kora dimau na wakili,
  • Uban Sarkin Zagi Bello na Yari
  • Ruwa da kada dibgau na Magaji
  • Sai tsohon wawa ka shigarsu.

Wannan waka da ya fara yi ita ce wadda ya yi wa tsohon sarkin Yamman Faru Ibrahim.

Dangane da yawan wakokin da Sa'idu Faru ya yi shi kansa ba zai iya kididdige yawansu ba.

Yaransa; - Mu'azu Daudun Kida (Dangaladima) - Dandaudu - Ali

Iyali: Makada Sa'idu Faru yana da mata uku da 'ya'ya da yawa da jikoki.

Don karin bayani sai a duba littafin MAKADA DA MAWAKAN HAUSA na Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]