Sadisu Abba Sawaba
Sadisu Abba Sawaba jarumi ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya Daɗe Yana fim a masana'antar yayi fina finai da dama a kanniwud.[1]
Takaitaccen Tarihin Sa.
[gyara sashe | gyara masomin]Cikakken sunan sa shine sadisu Abba Sawaba amma anfi sanin sa da said Sawaba , Haifaaffen jihar filato ne a garin jos. Ya shiga Masana'antar fim ta hanyar Dan uwa Kuma aboki s.b Mansur daga Nan ya fara fim , yayi fina finai da dama a masana'antar sannan Kuma fitattun fina finai a masana'antar.[2]
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]Yayi karatun firamare a St. Paul Primary School Jenta Jos, yayi karatun Sakandire a garin Jos, daga nan yazo Nuhu Bamalli Kaduna yayi karatu. Daga nan ya tafi Abubakar Tafawa Balewa bauchi , daga Nan ya tafi jami,ar Jos, ta karshen da yayi itace Ambrose Alli university edo. A yanzun haka shi malamin makaranta ne a makarantar kofar kudu primary school a jihar kaduna[3]