Jump to content

Salamatu Garba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Salamatu Garba

Salamatu Garba (An haife ta a watan Afrilu, shekara ta alif dari tara da sittin miladiyya 1960) a Jihar Kaduna. Yar gwagwarmaya ce.[1]

Ta yi karatun firamare a makarantar da ake kira da ( Our Lady’s Primary School) a cikin Jihar Kaduna, inda ta ci gaba da makaranta a matakin sakandare a (St. Faith’s College Kawo, Jihar Kaduna). Ta yi digirinta a [[Jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria a fannin rayuwar shuka. Ta yi digiri na biyu, a fannin, haka-zalika da kuma digiri na uku (doctorate degree) duk a Jami’ar Ahmadu Bello.[1]

Ta karantar a Jami’ar Ahmadu Bello daga shekarar alif dari tara da tamanin da hudu 1984 zuwa shekara ta alif dari tara da tamanin da tara 1989, kuma ta karantar a Jami’ar Bayero dake jihar Kano, daga shekarar 1990 zuwa shekara ta 1998. Ta kafa wata kungiya wadda za ta taimaka wa mata manoma a shekarar 1993. Ta yi aiki da UNICEF daga shekarar 2006 zuwa shekara ta 2008.[1]

  • Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
  • Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
  1. 1.0 1.1 1.2 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. p.p 184-185 ISBN 978-1-4744-6829-9.