Jump to content

Sarkin Daura Musa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sarauta a Zango

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan rasuwar sarkin Daura tafida a shekara ta 1905 a lokacin da aka zo zaɓen wanda zai gaje shi, sai masu naɗin sarauta, watau Kaura, Galadima, da Liman da Alkali da kuma Dan-sanwai suka yi shawarar yin kuri'a. Saboda haka sai aka tattara dukkan 'ya'yan Sarki domin su zo, su dauki kuri'a. aka yayyaga takardu, aka kudundune,amma daya ce kawai mai ci, kuma dan Sarkin da ya yi sa'ar daukar kuri'a mai ci ne zai zama Sarki. Sai Allah ya bai wa Mallam Musa sa'a ya ɗauki kuri'a mai ci , aka naɗa shi Sarki ya gaji Sarki Tafida.[ana buƙatar hujja]

Sarki Musa dan Sarki Nuhu ne, saboda haka shi kane ne ga Saarki Tafida. Sarki Musa malami ne mahardacin Al-qur'ani mai girma. A lokacin da aka nada Mallam Musa, Mr. H>R Palmer ne baturen da ke kula da kasar Daura, kuma yana zaune ne a Katsina. A cikin shekara ta 1904 ne aka kashe sarautar Baure,aka matar da kasar Baure karkashin Zango. [ana buƙatar hujja]

Bayan da aka hade Baure da Zango ne kuma Mr.Palmer ya fara shirin sake hade kasar Daura dukkanta a karkashin mulkin Mallam Musa. [1]

Sarauta a Daura

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 1906, Sarkin Daura Muhammadu Maigardoya rasu. Bayan rasuwarsa Maigardo, an nada dansa Bunturawa Sogaji ya gaje shi. Sogaji yayi kwana goma sha tara ne kadai Turawa suka fitar da shi, aka nada Magajiya Murnai, kanen Muhamman Miagardo. A wannan lokacin ne Sarkin Bai dan kauye ya kasaita. Shi bawan fulani ne kuma Sarki Miagardo ne ya fito da shi. Hasali ma dai, an yi imani da cewa Sarkin Bai Dankauye ya sa a tube Sogaji daga Sarauta.Ya kuma yi shirin da aka ba Magajiya Murnai Sarautar, Magajiya Murnai na auren diyar Sarkin Bai. A zamanin Magajiya Murnai ne aka nada Sarkin Bai Dankauye Wazirin Daura Magajiya Murnai bai dade bisa gadion mulki ba aka tube shi aka mayar da shi Sandamu. Waziri Dankauye kuma aka bashi rikon gari. Shima Waziri Dankauye bai dade ba yana rikon gari, akatube shi aka bai wa wani yaron Turawa mai suna Mallam Bawa rikon garin Daura.[2]

Dawowar Mallam Musa Garin Daura

A wannan lokacin ne Mr. Palmer ya bai wa Gwamna shawarar kashe sarautar Fulani a Daura da kuma maido Sarkin Zango Mallam Musa Dautra ya zama Sarkin dukkan kasar Daura. Gwamna Lugga ya amince da wannan shawara, aka maido da Mallam Musa bisa Gadon Sarautar Daura, wato sarautarsu ta iyaye da kakanni. [3] Mr. Palmer ne ya tabbatar wa Mallam Musa da sarautar Daura a cikin shekara ta 1906. Daurawa sun dawo gidan sarautarsu na asali kenan bayan gudun hijira na kusan shekara dari. [4]

Sarkin Daura Mallam Musa ya zauna lafiya tare da Fulani har zuwa lokacin da Allah ya yi masa rasuwa a cikin shekara ta 1911.

  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Daura_Emirate
  2. https://commons.wikimedia.org/wiki/File:Kofar_Sarki_Musa_Daura.jpg
  3. https://www.cambridge.org/core/journals/journal-of-african-history/article/abs/hausa-politics-the-affairs-of-daura-history-and-change-in-a-hausa-state-18001958-by-m-g-smith-berkeley-los-angeles-and-london-university-of-california-press-1978-pp-xix-536-illus-charts-etc-21/3FD9815F0566727DCD503915F0F80C36
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-11. Retrieved 2023-03-11.