Sashen Attiégouakro
Sashen Attiégouakro | |||||
---|---|---|---|---|---|
department of Ivory Coast (en) | |||||
Bayanai | |||||
Farawa | 2009 | ||||
Ƙasa | Ivory Coast | ||||
Babban birni | Attiégouakro (en) | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ivory Coast | ||||
District of Ivory Coast (en) | Yamoussoukro Autonomous District (en) |
Sashen Attiégouakro sashe ne na kasar Ivory Coast. Yana ɗaya daga cikin sassa biyu na gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta,
Yawan jama'a da ƙananan hukumomi
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da ƙidayar shekara ta 2021, Sashen Attiégouakro tana da yawan jama'a akalla mutum 49,513.[1] An raba sashen zuwa kananan hukumomi biyu, Attiégouakro da Lolobo.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]An kafa Sashin Attiégouakro acikin shekara ta 2009 a matsayin yanki na biyu a lokacin da aka raba Sashen Yamoussoukro na Lac zuwa gida biyu. [2]
A shekara ta 2011, an gabatar da gundumomin a matsayin sabbin yankuna na matakin farko a kasar Ivory Coast. Bugu da kari, an sake tsara yankunan sannan sun zama yanki na biyu sannan an mayar da dukkannin sassansu zuwa mataki na uku. A wannan lokacin, Sashen Attiégouakro ya zama wani yanki na gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta, ɗaya daga cikin gundumomi biyu a cikin ƙasar ba tare da yankuna ba.
Bayanan kula
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Citypopulation.de Population of regions and departments of Ivory Coast
- ↑ "Regions of Côte d'Ivoire (Ivory Coast)", statoids.com, accessed 16 February 2016.