Yamoussoukro
Yamoussoukro | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Suna saboda | Reine Yamousso (en) | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ivory Coast | |||
District of Ivory Coast (en) | Yamoussoukro Autonomous District (en) | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 355,573 (2014) | |||
• Yawan mutane | 101.59 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Bangare na | Eastern Plantations (en) | |||
Yawan fili | 3,500 km² | |||
Altitude (en) | 214 m | |||
Sun raba iyaka da |
Tiébissou Department (en)
| |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC±00:00 (en)
| |||
Lamba ta ISO 3166-2 | CI-YM | |||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | yamoussoukro.district.ci |
Yamoussoukro Birni ne, da ke a ƙasar Côte d'Ivoire. Shi ne babban birnin ƙasar Côte d'Ivoire. Yamoussoukro itace birni na biyar a yawan jama'a a Ivory Coast tare da akalla mutum 212,670, bisa ga jimillar shekarar 2014.[1] Tana da nisan kilomita 240km arewa maso yamma daga birnin Abidjan. Gundumar Yamoussoukro ta mamaye kasa mai fadin murabba'i 2,075sqkm (801 sq mi) tare da tuddai da kuma shararrun filaye.
Yamoussoukro ta zamo babban birnin kasar Ivory Coast a shari'ance acikin shekarar 1983, duk da cewa tsohuwar babban birnin har yanzu tana rike da sauran madakun iko. Kafin shekara ta 2011, inda kuma aka sani a yanzu a matsayin Yamoussoukro ta yau na daga cikin Lacs Region na da. An kuma kafa gundumar acikin shekara ta 2011[2] sannan kuma ta rarrabu zuwa sassa biyu; Sashen Attiégouakro da kuma SashenYamoussoukro. Gaba daya, akwai gidaje guda 169 a birnin. Yamoussoukro ta kasance karamar shiyya na Sashen Yamoussoukro sannan kuma kauye ce a sashen: tun daga shekara ta 2012, birnin Yamoussoukro ya zama muhimmin gari na Gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Tarihin baya
[gyara sashe | gyara masomin]Ana iya samu kayayyakin aiki yau da kullum wadanda aka kirkira kusan dubannan shekaru da suka gabata wanda ke nuna cewa akwai mazauna yankin Yamoussoukro tun zamunan iyaye da kakanni. A dalilin mamayewar Sahara, mafiya yawan mazauna sun gusa daga wurin saboda tsoron yanayin mara dadi.
Lokacin Mulkin Turawa
[gyara sashe | gyara masomin]Sarauniya Yamoussou, 'ya ga dan uwan Kouassi N'Go, tayi hijira zuwa garin N'Gokro a shekarar 1929 a lokacin mulkin turawan Faransa. An sauya wa kauyen N'Gokro suna zuwa Yamoussoukro, kalmar Kro na nufin kauye a harshen Baoulé.
Daga nan, an kulla alaka ta kasuwanci da kuma siyasa a wannan lokacin, amma a shekarar 1909, ka'idar da Djamlabo "Akoué" ya bada ya janyo adawa da wannan gwamnatin. An cinna wa tashar Bonzi wuta wanda ke da nisan kilomita 7km (4.3 mi) daga Yamoussoukro dake kan titin Bouaflé, sannan da kyar aka cece mai gudanarwa dan kasar Faransa a dalilin Kouassi N'Go da ya kwace sa.
A yayinda abun yayi ƙamari, Maurice, ganin cewa an samu zaman lafiya Bonzi, ya yanke shawarar tura da sojojin Faransa zuwa Yamoussoukro inda gwamnatin Faransa ta gina hasumiya don tunawa da Kouassi N'Go, 'yan tawayen Akoué sun kashe shugaban Akoué a shekarar 1910, suna zarginsa da cewa ya kuma cika shigewa turawan Faransa.[3]
A shekarar 1919, an soke tashar farar hula ta Yamoussoukro. Félix Houphouët-Boigny ya zamo shugaban Yamoussoukro a shekarar 1939. Yamoussoukro ta wanzu tsawon shekaru da dama a matsayin garin noma. Hakan ya cigaba har zuwa shekarar Yakin Duniya na BIyu, lokacin da aka kirkiri Kungiyar Noma ta Afirka, dangane da taron jagororinta na farko. Amma sai bayan samun 'yancin kai ne Yamoussoukro ta fara bunkasa.[4]
A shekarar 1950, akwai mazauna 500 a kauyen.[5]
Bayan samun 'yancin kai
[gyara sashe | gyara masomin]Bayan shekarar 1964, shugaban kasa Félix Houphouët-Boigny ya tsara burika kuma ya fara aiki akan su. Wata rana, acikin shekarar 1965, wanda daga baya ake kira Babban Darasin Yamoussoukro, ya kuma ziyarci gonar tare da shugabannin lardin, yana gayyatarsu da su kai wadannan dabaru na noma zuwa yankunansu. A ranar 21 ga watan Yulin shekarar 1977, Houphouët ya sadaukar da gonakinsa ga Jiha.
Acikin watan March na shekarar 1983, shugaban ƙasa Houphouët-Boigny ya mayar da Yamoussoukro babban birnin siyasa da gudanarwa na kasar Ivory Coast, kasancewar a garin aka haifeshi.[6] Hakan ya zamo canjin babban birnin kasan na hudu acikin karni guda. Manyan biranen Ivory Coast na baya sune Grand-Bassam (1893), Bingerville (1900), da kuma Abidjan (1933).
An gina birnin Yamoussoukro a shekara ta 1983.
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Yamoussoukro - panoramio
-
Wani Abinci a Yamoussoukro, Code d'Ivoire
-
Wata mata na dafa abinci a birnin
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ivory Coast: Districts, Major Cities & Localities - Population Statistics, Maps, Charts, Weather and Web Information". www.citypopulation.de. Retrieved 12 February 2023.
- ↑ Décret n° 2011-263 du 28 septembre 2011 portant organisation du territoire national en Districts et en Régions.
- ↑ Coates, Carrol F. (1 January 2007). "A Fictive History of Côte d'Ivoire: Kourouma and "Fouphouai"". Research in African Literatures. 38 (2): 124–139. doi:10.2979/RAL.2007.38.2.124. JSTOR 4618379. S2CID 161600527.
- ↑ Braimah, Ayodale. "Yamoussoukro, Cote d'Ivoire (1909– )". BlackPast.org. Archived from the original on 14 September 2018. Retrieved 8 September 2017.
- ↑ Cyril K. Daddieh, Historical Dictionary of Cote d'Ivoire (The Ivory Coast), Rowman & Littlefield, USA, 2016, p. 490
- ↑ Roman Adrian Cybriwsky, Capital Cities around the World: An Encyclopedia of Geography, History, and Culture, ABC-CLIO, USA, 2013, p. 339